Hotuna: Jirgin Ƙasar Kaduna zuwa Abuja Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Hastari a Hanya

Hotuna: Jirgin Ƙasar Kaduna zuwa Abuja Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Hastari a Hanya

  • Hankula sun tashi yayin da jirgin kasa da ya taso daga tashar jirgi ta Rigasa, a jihar Kaduna ya yi hatsari a kan hanyar zuwa Abuja
  • Wannan na zuwa ne mako guda bayan wani jirgin AKTS dauke da fasinjoji ya samu matsala lokacin da ya baro tashar Kaduna
  • A hatsarin na yau Talata, 26 ga Agusta, wani fasinja ya bayyana irin halin da fasinjoji suka shiga lokacin da taragon jirgin suka kife

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Fasinjoji sun shiga cikin tsananin tashin hankali yayin da jirgin kasa ya yi hatsari a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

An ce jirgin da ya kwaso fasinjoji daga tashar jirgi ta Rigasa, Kaduna, a hanyar zuwa Abuja, ya sauka daga kan layinsa, inda wasu taragonsa suka kife.

Kara karanta wannan

Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya

Jirgin kasa da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari.
Hotunan hatsarin jirgin kasa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, an ga yadda tarago ya wuntsula daga kan hanyarsa. Hoto: @miskayofficial
Source: Twitter

Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya yi hatsari

Wannan hatsarin dai ya afku ne a safiyar ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, kuma ya jefa fasinjoji cikin firgici da neman tsira, inji rahoton Aminiya.

Wani fasinja da ya tsira daga hatsarin, ya ce dukkanin fasinjoji sun shiga firgici, kowannesu ya rika neman hanyar tsira a lokacin da abin ya faru.

Har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto ba a tabbatar da abin da ya jawo hatsarin ko kuma yawan mutanen da ke cikin jirgin ba.

Jirgin kasa da ke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sha fuskantar hadari da kuma cikas a zirga-zirgarsa, ciki har da harin 'yan bindiga na watan Maris din 2022.

Hukumomi ba su kai ga fitar da sanarwa game da wannan hatsarin na ranar Talata ba.

Lalacewar jirgin Kaduna-Abuja a makon jiya

A makon da ya gabata, SaharaReporters ta rahoto cewa hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wani jirgin kasa ya gamu da matsala.

Kara karanta wannan

JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi

NRC ta ce an gano kafafuwan daya daga cikin taragon jirgin Abuja-Kaduna (AKTS) ya gamu da matsala, inda ya dauki zafi sosai sakamakon gugar karfe a yammacin Laraba.

A cewar sanarwar da jami'in hulda da jama'a na NRC, Callistus Unyimadu ya fitar, hukumar ta ce an gano matsalar kilomitoci kadan bayan jirgin ya bar tashar Rigasa.

An ce zafin da kafafuwan ko tayoyin jirgin suka yi, ya faru ne sakamakon sauyin yanayi da kuma tsananin zafin gugar kafafuwan da layin dogo.

Jirgin da ya yi hatsari a safiyar Talata ya kwaso fasinjoji ne daga tashar jirgi ta Rigasa, Kaduna
Daya daga cikin jiragen kasan Najeriya da ke aiki a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Matakin da NRC ta dauka kan jirgin kasan

A cikin sanarwar, Unyimadu ya yi nuni da cewa an dauki matakin gaggawa bayan da aka gano matsalar, inda aka mayar da jirgin zuwa Kaduna.

Biyo bayan wannan ne NRC ta ce za a samu 'yar tangarda ta yawan fasinjojijin da za a dauka, musamman fasinjojin da suke a rukunin 'yan kasuwa.

Hukumar ta bayar da hakuri kan wannan matsala da aka samu, yayin da aka gyara jirgin kuma ya ci gaba da hada-hadar fasinjoji.

Kafar watsa labarai ta Arise News ta wallafa hotunan hatsarin da jirgin kasan ya yi a ranar Talata, kalli hotunan a kasa:

Kara karanta wannan

Abin da ya sa aka dauke sabis din MTN a Kano da wasu jihohi 2 a Arewacin Najeriya

Tinubu zai gina layin dogo a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya za ta gina titin jirgin kasa a Kano wanda zai rage cunkoson abubuwan hawa a birnin.

Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Kabir Bichi ya ce aikin zai ƙara daraja ga tattalin arzikin jihar Kano da ma Arewacin Najeriya baki daya.

Hon. Abubakar Kabir Bichi ya ce shirin yana cikin muhimman ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar a Arewacin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com