Kaduna-Abuja: An sace mutane, an jikkata wasu a tashar jirgin Rigasa

Kaduna-Abuja: An sace mutane, an jikkata wasu a tashar jirgin Rigasa

Labari ya iso mana cewa ‘Yan bindiga sun kai hari kan motocin wasu Bayin Allah da ke kokarin shiga tashar jirgin kasa da ke Garin Kaduna.

Wadannan ‘Yan bindiga sun kai wannan hari ne a Ranar Asabar a lokacin da mutanen su ka isa tashar jirgin na zuwa Abuja wanda ke Rigasa.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta bayyana cewa an kai harin ne a kan titin da ya hada hanyar filin jirgin sama da tashar dogon.

An kai wannan hari ne da kimanin karfe 8:00 na dare. Wannan shi ne hari na biyu da aka kai a cikin ‘yan kwanakin nan inji Jaridar The Cable.

An kai makamancin irin wannan hari a Rigasa a Ranar Juma’a cikin dare. Yanzu haka ana neman kudi daga hannun Iyalin wadanda aka sacen.

KU KARANTA: Jami'ai sun hana wasu 'Yan Matan Najeriya 9 tashi a filin jirgi

Kaduna-Abuja: An sace mutane, an jikkata wasu a tashar jirgin Rigasa
An matsawa Matafiyan Abuja zuwa Kaduna da hare-hare
Asali: Depositphotos

‘Yan bindigan sun bukaci a biya su kudi Naira miliyan 20 kafin su saki wani fasinja da su ka yi garkuwa da shi a harin karshen makon jiyan.

Haka zalika wani daga cikin wadanda aka harba da bindiga ya na asibitin Sojoji na 44 inda ake duba lafiyar sa kamar yadda mu ka samu labari.

Wani wanda abin ya faru gabansa ya bayyana cewa bayan jama’a sun ji karar bindiga, sai su ka yi maza su ka koma cikin motocinsu, su ka ruga.

“An yi irin haka a Ranar Juma’a da dare, haka zalika sun sake kai wa Matafiya hari a daren Ranar Asabar.” Wani ya shaidawa ‘Yan jarida.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da wannan hari, inda ya ce za su fito su yi jawabi a kai nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng