'Sama da Kungiyoyi 1,000,' Gambari Ya Tono Tarin 'Yan Ta'ddan da ke cikin Afrika

'Sama da Kungiyoyi 1,000,' Gambari Ya Tono Tarin 'Yan Ta'ddan da ke cikin Afrika

  • Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce sama da kungiyoyin ta’addanci 1,000 ke aiki a Afrika
  • Ya yi kira ga shugabannin nahiyar da su gina masana’antar tsaro da fasahar kansu don fuskantar barazanar da ke damun yankinsu
  • Farfesa Gambari Ya fadi haka ne a wani taron tsaron Afrika da aka gudanar Abuja tare da halartar kasashe 36 daga cikin 54 na nahiyar Afrika

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a zamanin marigayi Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari ya yi magana kan tsaro.

Ya bayyana cewa akwai kungiyoyin ta’addanci da dama a nahiyar Afrika, inda ya ce mafi yawan wadannan kungiyoyi na da hatsarin gaske ga rayuka da tsaron kasashen nahiyar.

Kara karanta wannan

Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya

Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Gambari
Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Gambari. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Gambari ya yi wannan jawabi ne a yayin taron farko na manyan hafsoshin tsaro na kasashen Afrika da aka gudanar a Abuja.

Ya shawarci kasashen nahiyar da su tashi tsaye wajen samar da masana’antun tsaro da kuma kirkirar fasahohi domin gina tsarin tsaro na Afrika da zai kare mutane.

Yaduwar 'yan ta'adda a nahiyar Afrika

A tarihinsa, Farfesa Gambari ya taba rike mukamin ministan harkokin wajen Najeriya da wakilin dindindin na kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana cewa 'yan ta'adda suna da kungiyoyi sama da 1,000 a nahiyar Afrika.

Yayin da ya ke jawabi, ya ce akwai bukatar kowace kasa ta fara tabbatar da tsaron cikinta kafin a koma matakin kare sauran yankuna da nahiyar baki daya.

Ya bayyana cewa Najeriya ta kasance a sahun gaba wajen kare yankin saboda rawar da ta ke takawa wajen yaki da ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a yankin Sahel da yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Babu zama: Kwankwaso ya dura Legas bayan ruguza kasuwar Hausawa

'Yan Afrika da suka halarci taron

Rahotanni daga taron sun tabbatar da cewa daga cikin kasashe 54 da aka gayyata, kasashe 36 ne suka halarta.

Wakilan Jamhuriyar Nijar sun halarci taron, amma kasashen Mali da Burkina Faso ba su hallara ba, abin da ake ganin ba zai rasa nasaba da takaddama tsakaninsu da kungiyar ECOWAS ba.

Rashin halartar ya kara nuna rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Yammacin Afrika, musamman bayan juyin mulkin soji da ya faru a wadannan kasashe a shekarun baya.

Tawagar Najeriya wajen taron tsaron Afrika a Abuja
Tawagar Najeriya wajen taron tsaron Afrika a Abuja. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Bukatar hadin gwiwar tsaro a Afrika

A nasa bangaren, hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa barazanar da ke addabar nahiyar za ta iya shafar kowa, don haka akwai bukatar hadin gwiwa.

Vanguard ta rahoto ya ce dole ne kasashen nahiyar su kara shiri kan tsarin tsaronsu da kansu ba tare da dogaro da kasashen waje ba, domin ba kowa zai kare su ba sai su da kansu.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

Janar Musa ya kara da cewa sojojin Najeriya suna da shirin yin aiki tare da takwarorinsu na kasashen Afrika domin dakile ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.

An saya wa mutane makamai a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa 'dan majalisar jihar Katsina da ke wakiltar Funtua ya sayawa mutanensa bindigogi.

'Dan majalisar ya bayyana cewa ya saya musu makaman ne domin kare kansu daga sharrin 'yan bindiga masu garkuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen yankin Funtua sun dade suna bukatar a saya musu makamai kuma sun yi farinciki da hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng