Badakalar N6.5bn: Gwamnatin Kano Ta Bar Manyan Lam'a wajen Wanke Hadimin Abba

Badakalar N6.5bn: Gwamnatin Kano Ta Bar Manyan Lam'a wajen Wanke Hadimin Abba

  • Gwamnatin Kano ta fara fuskantar zazzafar suka daga masu sharhi kan kare guda daga cikin hadiman Abba Kabir Yusuf
  • Wani rahoto da ya fito a 'yan kwanakin baya ya zargi Daraktan Kula da Harkokin Fadar Gwamnatin Kano, Abdullahi Rogo da badakalar N6.5bn
  • A sanarwar da gwamnatin ta fitar ta kare shi, jama'a sun fara nuna kura kuran dake tattare da kokarin da aka yi na wanke shi daga zargin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano na fuskantar suka daga jama’a da masana kan yadda ta mayar da martani kan zarge-zargen almundahana da aka alakanta da hadiman gwamna, Abdullahi Rogo.

Wani rahoto da aka fitar a baya bayan nan ya yi zargin cewa Daraktan Kula da Harkokin Fadar Gwamnatin Kano, Abdullahi Rogo, ya wawure N6.5bn, kuma batun yana gaban kotu.

Kara karanta wannan

Babu zama: Kwankwaso ya dura Legas bayan ruguza kasuwar Hausawa

Ana musayar yawu kan sanarwar gwamnatin Kano kan hadimin Abba
Hoton gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da hadiminsa, Abdullahi Rogo Hoto: Aliyu Jalal
Source: Facebook

Aliyu Jalal, wani marubuci kuma mai sharhi a kan al'amura, ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce gwamnatin Kano ta rude.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara sukar gwamnatin jihar Kano

Aliyu Jalal ya bayyana cewa sanarwar da gwamnati ta fitar jawabi ne marar amfani, yake cewa sam ba jawabin da ya kamata a yi wa jama'a kenan ba.

Sanarwar da ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta ce gwamnati na da yakinin Abdullahi Rogo bai yi almundahanar da ake zargi ba.

Amma a sakon, Aliyu Jalal ya ce:

“Sun ce za su kawo hujjoji dalla-dalla amma babu ko guda. Sun mayar da hankali ne wajen dora laifi kan abokan adawa da kuma yabon Gwamna Abba Kabir Yusuf.”

Ya kara da cewa sanarwar ta kasa kawo lambar kwangila, takardun biyan kudi ko lambobin kasafin kudi da za su tabbatar da sahihancin kariyar da gwamnati ke baiwa Rogo ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya kirkiro sababbin sarakuna 3, ya dawo da Sarki kan mulki

A rubutun da ya yi, Jalal ya jero kura-kurai da aka yi a yunkurin wanke Rogo daga zargi, inda a karshe aka koma zargin 'yan jarida da sukar gwamnatin APC.

Abba Hikima ya magantu kan gwamnatin Kano

Shi ma fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima, ya yi tsokaci a shafinsa na Facebook, ya soki yadda gwamnatin Kano ta dauki lamarin.

Abba Hikima ya soki gwamnatin Kano
Hoton Abba Kabir Yusuf (D), Abba Hikima (H) Hoto: Ibrahim Adam/Abba Hikima
Source: Facebook

Ya ce:

“Zarge-zargen cin hanci da rashawa ne yasa muka yaki gwamnatin Ganduje. Saboda haka idan aka zargi gwamnatin Abba Gida-Gida da rashawa… dole ta kare kanta da hujjoji ko ta binciki kuma ta hukunta wadanda ake zarg."

Abba Hikima ya jero wasu batutuwa da ke bukatar bayani, ciki har da cewa wanda ake zargi ya amsa laifi da kansa, kotu ta kwace wasu kudi daga hannunsa.

Ya ce:

“Aikin ‘yan adawa shi ne su fitar da zarge-zarge, amma aikin gwamnati shi ne kare kanta da hujjoji ko gyara kura-kurai."

Masu sharhi sun yi gargadin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf, wadda ta yi yakin neman zabe da kudirin yaki da rashawa, tana cikin hadarin rasa goyon bayan jama'a kan batun.

Kara karanta wannan

'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge

A bayanin da ka yi, an yi watsi da batun cewa ICPC da EFCC suna binciken Rogo bayan ganin biliyoyi a asusunsa kuma har an yi nasarar dawo da wasu kudi.

Gwamnatin Kano ta kare hadimin Abba

A wani labarin, mun wallafa cewa ofishin mai magana da yawun gwamnan Kano ya musanta zargin da jaridar Daily Nigerian ta yi cewa wani daga cikin hadiman gwamna.

Mai magana da ywaun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin ya fitar da sanarwar da ta kare Daraktan kula da ayyukan fadar gwamnati, Abdullahi Rogo daga zargin wawure N6.5bn daga asusun jihar.

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta kuma jawo hankalin jama’a ga irin almubazzarancin kuɗi da ake zargin gwamnatin da ta gabata na satar Naira biliyan 20 a wata uku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng