'Kowa Ya Shirya,' Ana Fargabar Ambaliya za Ta Shafi Yankuna 14 a Jihohin Arewa 9

'Kowa Ya Shirya,' Ana Fargabar Ambaliya za Ta Shafi Yankuna 14 a Jihohin Arewa 9

  • Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar da gargadi cewa jihohi tara da yankuna 14 a Arewa na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin 25 zuwa 29 ga Agustan 2025
  • Gargadin ya fito daga Cibiyar Gargaɗi kan Ambaliya, inda aka bukaci mazauna kauyuka a gabar Kogin Neja daga Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta barin yankunan
  • Jihohin da abin zai shafa sun hada da Adamawa, Borno, Gombe, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, inda aka bayyana kauyuka da dama cikin hatsarin ambaliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabon gargadi na yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi tara na Arewacin Najeriya da kuma wasu yankuna 14 da ke fuskantar barazanar ruwan sama.

Cibiyar Gargaɗi kan Ambaliyar Ruwa ta Ma’aikatar Muhalli ta bayyana cewa ruwan sama da ake sa ran samu tsakanin 25 zuwa 29 ga Agustan 2025 ne ka iya haddasa ambaliyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ambaliyar ruwa ta shiga gidaje 4521 a jihar Yobe, an rasa rayuka

Yadda aka yi ambaliyar ruwa a Borno a 2024
Yadda aka yi ambaliyar ruwa a Borno a 2024. Hoto: Imrana Muhammad
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa takardar da ma'aikatar ta fitar ta bukaci jama’a musamman mazauna da ke kusa da Kogin Niger daga Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta barin yankunan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohi 9 da aka ce za a yi ambaliya

Jihohin da aka yi hasashen za su iya fuskantar ambaliya sun hada da:

  • Adamawa (Abba-Kumbo, Mubi, Shelleng)
  • Bauchi (Azare)
  • Borno (Ngala)
  • Gombe (Nafada)
  • Jigawa (Gwaram)
  • Kano (Sumaila)
  • Katsina (Bindawa, Kaita, Katsina)
  • Sokoto (Makira)
  • Zamfara (Anka)

Ma’aikatar ta ce ruwan sama mai yawa zai iya kawo ambaliyar da za ta lalata gidaje, gonaki da hanyoyin sadarwa.

Barazanar kwararar ruwa a kogin Niger

Sanarwar ta ce sakamakon karuwar ruwan Kogin Niger, akwai bukatar jama’a da ke zaune a kusa da kogin daga Jebba har zuwa Lokoja da su fice daga gidajensu domin kauce wa hadari.

Ya kara da cewa a kwanakin baya ma’aikatar ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihohi bakwai da wurare 25 a fadin kasar, inda aka ga alamu na karuwar ruwan sama da ya zarce kima.

Kara karanta wannan

NiMet ta yi hasashen ruwan sama da guguwa na kwana 3 a Kano da sassan Najeriya

Yayin da ake fargabar ambaliya a jihohi tara, jihar Yobe ta riga ta gamu da mummunar ambaliya a makonnin baya, inda gidaje 102 suka lalace, yayin da aka raba mutane 612 da muhallansu.

Jami'an NEMA sun kai agajin gaggawa yayin wata ambaliya
Jami'an NEMA sun kai agajin gaggawa yayin wata ambaliya. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Twitter

Kira ga jama’a kan ambaliyar ruwa

Punch ta ce gwamnati ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da yin biyayya ga umarnin da hukumomi suka bayar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka kuma, ta shawarci shugabannin al’umma da su wayar da kan jama’a kan muhimmancin ficewa daga yankunan da ake hasashen ambaliya, domin kare rayukan su kafin aukuwar bala’i.

Za a yi ruwa na kwana 3 a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa, NiMet ta yi hasashen cewa za a shafe kwana uku ana ruwa a jihohin Najeriya.

NiMet ta bayyana cewa ruwan zai shafi dukkan sassan Najeriya da suka hada da jihohin Kudu da Arewa.

Ta gargadi jama'a da su kaucewa shiga karkashin bishiya a lokacin da aka fara ruwan domin kubutar da rayuwar su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng