JIBWIS Ta Ƙalubanci Masu Cewa an Yi Wa Jingir Ihu a Abuja, Ta Sanya Kyautar Kuɗi
- An yada jita-jita cewa an yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir ihu a masallacin Abuja, amma masoyansa sun ƙaryata lamarin da suka kira sharri
- Kungiyar JIBWIS reshen Gombe ta kalubalanci masu yada wannan zargi, inda ta ce za ta ba da kyauta ga duk wanda ya kawo hujjoji
- JIBWIS ta sanar da kyautar N500,000 ga duk wanda ya kawo bidiyo, murya ko shaidu na da ke tabbatar da abin ya faru
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A Najeriya, an yi yada jita-jitar cewa an yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir ihu a masallacin Abuja.
Majiyoyi suka ce an yi wa malamin ihu ne yayin da yake wa'azi kafin daga bisani ya koma maganar siyasa.

Source: Facebook
Shafin JIBWIS reshen jihar Gombe ya kalubalanci masu yada wannan karya a jiya Litinin 25 ga watan Agustan 2025 a manhajar Facebook.

Kara karanta wannan
'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jingir ya saba yabon gwamnatin Bola Tinubu
Sheikh Jingir na daga cikin malamai ko a ce na gaba gaba da ke goyon bayan Bola Tinubu tun kafin zaben 2023.
Malamin ya sha bayyana cewa yana goyon bayan Tinubu da Shettima ne saboda kishin Musulunci.
An zaɓi Tinubu da Shettima karkashin jam'iyyar APC wanda dukansu Musulmi ne lamarin da ya ta da jijiyoyin wuya a fadin Nigeria baki daya.
Yadda tikitin Muslim/Muslmi ya ta da kura
Tikitin Musulmi da Musulmi ya jawo maganganu yayin da ake kamfe a zaben 2023 har zuwa yanzu da ake tunkarar 2027.
Har yanzu akwai wasu da ke ganin ya kamata a sauya Kashim Shettima a zabi wani Kirista daga yankin Arewacin Najeriya.
Sai dai duk da haka akwai wadansu da ke ganin sauya Shettima zai iya kawo matsala a zaben 2027 saboda addini.

Source: Facebook
Maganganu sun biyo bayan yi wa Jingir ihu
Bayan yada cewa an yi wa Jingir ihu, masoyansa da dama sun ƙaryata lamarin da suke cewa sharrin makiya ne.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa kan aihinin gaskiyar abin da ya faru wanda bai yi wa masoyansa dadi ba.
Daga bisani JIBWIS a Gombe ta ce za ta ba da kyautar makudan kudi ga wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ajiye N500, 000 ga duk mahalukin da ya kawo bidiyo ko murya lokacin da aka yi wa Sheikh Jingir ihu.
Sanarwar ta ce:
"Ihu a Masallacin Guzape Abuja,
"Kyautar N500k kyauta ga duk wanda ya kawo bidiyo, murya ko kuma wanda ya gani da idonsa akan faruwar abin."
Gaskiyar lamari kan yiwa Jingir ihu a Abuja
Mun ba ku labarin cewa kungiyar Izala ta yi karin haske kan zargin cewa an yi wa shugaban malaman ta, Sheikh Sani Yahya Jingir, ihu a Abuja.
A bayani da wani jagora a Izala ya fitar, kungiyar ta ce labarin karya ne kuma sharrin masu neman bata suna ne.
Ta yi kira ga Musulmai su rika binciken kowane labari kafin yada shi, kamar yadda Alkur’ani ya yi umarni da hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
