Tashin Hankali: Ambaliyar Ruwa Ta Shiga Gidaje 4521 a Yobe, An Rasa Rayuka
- Akalla mutane bakwai suka mutu yayin da wasu 12,470 suka rasa muhallansu a lokacin da ambaliyar ruwa ta afkuwa a Yobe
- Ambaliyar ruwan ta afku ne a ranar 15 da 17 ga watan Agusta, 2025 a garuruwa daban daban na jihar, inda ta shafi gidaje 4,521
- SEMA ta bayyana cewa gwamnatin Yobe na aiki tare da YOGIS da sauran hukumomi, don ba ba da agaji da daukar matakan gaggawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Mummunar ambaliyar ruwa ta afku ba zato ba tsammani a wasu garuruwan jihar Yobe, inda ta yi barna a akalla gidaje 4,521.
Ambaliyar, wacce ta afku bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi a sassan Arewa maso Gabashin Yobe ta yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.

Kara karanta wannan
APC ta shiga matsala, magoya bayan jam'iyyar 50,000 sun sauya sheka zuwa ADC a Sokoto

Source: Getty Images
Ambaliyar farko ta taba mutane 12,470
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha (SEMA), Mohammed Goje, ya bayyana hakan yayin ganawa da 'yan jarida a Damaturu, inji rahoton Channels TV.
Ya ce an ɗauki matakan gaggawa da suka haɗa da ciyar da wadanda ambaliyar ta shafa da samar masu da matsugunni na wucin gadi, hade da duba lafiyarsu da kuma gudanar da binciken gaggawa kan lamarin.
Mohammed Goje ya ce:
“A ranar 15 ga Agusta, 2025, ambaliya ta afku a karamar hukumar Potiskum, inda ta shafi unguwanni 21 a cikin mazabu biyar, ta kuma tilasta mutane 12,470 barin gidajensu.
“Cikin ‘yan sa’o’i kaɗan, SEMA ta ɗauki matakan gaggawa, ciki har da ciyar da mutanen, samar masu da matsugunni, ba su tallafin lafiya.'"
Yobe: Ambaliya ta 2 ta shafi mutane 2,937
Shugaban hukumar SEMA ya ce kaso 85 na gidajen da ambaliyar ta yi wa mummunar barna ginin kasa ne, kuma mutane sun samu duk wani taimako na gaggawa.
“Haka nan, a ranar 17 ga Agusta, mun samu kiran gaggawa na afkuwar ambaliya a karamar hukumar Nangere, inda ta shafi mutane 2,937 a garuruwan Garin Kolo da Ajim.
"Hukumar SEMA ta tura tawagar ma’aikata da masu aikin ceto domin taimakon mutanen da ambaliyar ta shafi gidajensu 550.
“Matakan gaggawar da aka dauka sun haɗa da gina karamar katangar kariya da jakunkunan yashi, ba da agajin abinci, samar da ruwan sha mai tsafta, da sauran kayayayyaki na tsafta don kauce wa barkewar cututtuka.”

Source: Getty Images
Jihar Yobe ta dauki matakai kan ambaliya
Mohammed Goje ya bayyana cewa hukumar tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin jihar, musamman hukumar YOGIS, domin hana mutane gina gidaje a kan hanyoyin ruwa.
Haka zalika, gwamnatin ta kaddamar da tsarin sa ido kan kwararowar ruwa daga kogunan Yobe, Komadugu, Katagum da Hadejia.
Wannan ya biyo bayan gargadin da NiMet da NIHSA suka yi wa kananan hukumomin da ke da haɗarin ambaliya yayin da ake hasashen saukar ruwa mai yawa.
Ambaliya: Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohi 7
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta yi hasashen ambaliya a jihohi bakwai, inda ta gargadi mazauna bakin kogin Jebba zuwa Lokoja.
Sanarwar ta bayyana cewa jihohin da abin zai shafa sun hada da Benue, Borno, Gombe, Kebbi, Nasarawa, Neja da kuma Yobe.
Hukumar NEMA ta yi kira ga mazauna wasu garuruwan Kebbi, Neja da Kwara da su kaura daga gidajensu don kare kai daga ambaliya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

