Abin da Ya Sa Aka Dauke Sabis Din MTN a Kano da Wasu Jihohi 2 a Arewacin Najeriya
- Kamfanin sadarwa na MTN ya dawo da sabis mai karfi a kananan hukumomi 15 da ke jihohin Kano, Adamawa da Borno
- An dan samu katsewar sabis na MTN a wadannan yankuna ne sakamakon lalata wata hanyar sadarwa, wacce kamfanin ya gyara ranar Lahadi
- Kamfanin ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kokarin inganta ayyukansa da samar da sabis mai inganci a a fadin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya bayyana cewa ya kammala aikin gyaran hanyoyin sadarwa wanda ya shafi wurare 101 a kananan hukumomi 15 da ke jihohin Adamawa, Borno da Kano.
Kamfanin ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, yana mai tabbatar da cewa sabis ya dawo a wuraren da lamarin ya shafa.

Source: UGC
MTN Najeriya ya ce hakan ya nuna kokarin da yake na tabbatar da ingancin sabis din waya a Arewa maso Gabas duk da matsalar tsaron da ake fuskanta, rahoton Daily Trust.
A cikin sanarwa da kamfanin ya fitar, MTN ya ce aikin ya zama dole ne sakamakon yawan yanke igiyoyin sadarwa da kuma lalata kayan aiki da ake fuskanta a Arewa maso Gabas.
Matsalar da MTN ya samu a wasu jihohi
Ya ce gyaran, wanda aka yi a jiya Lahadi, 24 ga watan Agusta, 2025, ya shafi sabon turken sadarwa da aka kafa a kan hanyar AFCOT zuwa kauyen Bawo a Jihar Adamawa.
Sanarwar ta ce:
“Wannan aiki ya zama dole domin gyara igiyar sadarwar da ta lalace a baya. An kammala aikin gyaran cikin lokacin da aka tsara, kuma an dawo da sabis kafin karfe 1:00 na rana a ranar Lahadi, 24 ga Agusta.”
Kamfanin MTN ya kara da tabbatar da cewa sabis ya dawo da karfinsa a duka kananan hukumomin da wannan gyara ya shafa a Kano, Borno da Adamawa.
Kamfanin MTN ya bayar da hakuri
"Muna tabbatar wa wadanda lamrin ya shafa cewa komai ya dawo daidai, sabis ya dawo yadda ya kamata. Muna kara godewa kwastomomin mu tare da ba su hakurin dan lokacin da aka dauka babu sabis," in.ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa sabis da wannan matsala ta shafa sun hada da 2G, 3G, 4G amma duka an yi nasarar gyara su, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Source: Getty Images
Yankunan da matsalar MTN ta shafa a Kano da jihohi 2
Kananan hukumomin da aka dauke sabis na dan lokaci su ne, Girei, Song, Mubi North, Hong da Michika a Adamawa; Askira/Uba da Shani a Borno; da kuma Nasarawa a Kano.
Kamfanin MTN ya ce an tsara aikin gyara ne da tsakar rana don kare lafiyar injiniyoyin saboda yanayin tsaro, kuma komai ya kammala.
MTN ya ce wannan gyara na cikin shirinsa na karfafa tsarin sadarwar a yankunan da ba su da wadataccen sabis, tare da tabbatar da samar da sabis mai inganci a duk fadin Najeriya.
Kamfanonin sadarwa sun yi gargadi a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa kamfanonin sadarwa a Najeriya sun koka kan yadda ake lalata kayan aikinsu a jihohi 17 a Najeriya.
Sun yi gargaɗin cewa matukar aka ci gaba da kai hare-hare tare da sace kayayyakinsu, za a fuskanci tangarɗar hanyoyin sadarwa.
Kamfanonin sun buƙaci dakarun tsaron Najeriya su taimaka wajen kare turakan sadarwa domin gujewa rashin karfin intanet da ɗaukewar sabis a wasu yankuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

