Ba Sani ba Sabo: Gwamnatin Tinubu Ta Rufe Kwalejojin Bogi 22 a Najeriya
- Hukumar NCCE ta gano tare da rufe kwalejojin koyar da malamai 22 da ke aiki ba bisa doka ba a fadin Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin ilimi da su kawar da duk wata babbar makarantar bogi da a kasar
- Gwamnati ta ce tana aiki don karfafa hadin kai tsakanin hukumomin ilimi domin inganta tsarin karatun Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar kula da kwalejojin koyar da malamai a Najeriya, wato NCCE, ta sanar da rufe kwalejoji 22 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na kasar.
Hakan ya zo ne a wani samame da hukumar ta gudanar kan makarantun bogi da ake amfani da su wajen cutar da al'umma.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa rahoton nasarorin da hukumar ta gabatar ya tabbatar da wannan mataki, wanda aka ce ya zama wajibi don kare martabar ilimi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin da hukumar NCCE ta samu
Hukumar ta ce baya ga rufe kwalejojin bogi, ta gudanar da bincike kan ma’aikata da kuma sa ido kan harkokin kudi a dukkan manyan kwalejojin koyar da malamai 21 na tarayya a Najeriya.
The Guardin ta rahoto cewa matakin ya nuna cewa hukumar ba wai kawai ta tsaya ne kan gano makarantun bogi ba, har ma tana tabbatar da bin ka’idojin aiki a makarantun gwamnati.
Umarnin shugaba Tinubu kan ilimi
A baya-bayan nan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga hukumomin ilimi da su tsananta yaki da makarantun bogi da ke bata tsarin ilimi.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya bayyana haka ne a yayin bikin kammala karatu karo na 14 na jami'ar NOUN da aka gudanar a Abuja.
Shugaban, wanda wakiliyarsa, Rakiya Ilyasu ta isar da sakon nasa, ya ce ba za a lamunci lalata nagartar tsarin ilimi ba domin gudun ruguza makomar daliban Najeriya.
Tinubu ya nemi inganta ilimi a Najeriya
Tinubu ya jaddada cewa gwamnati tana da kudurin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin da ke kula da ilimi domin inganta harkokin karatu.
Ya ce hukumomin JAMB, NYSC, NUC, NBTE da NCCE suna aiki tare wajen ganin an kawar da batun takardun bogi da kuma makarantu marasa sahihanci a Najeriya.

Source: Twitter
Tasirin matakin ga tsarin ilimin Najeriya
Rufe kwalejojin bogi 22 da NCCE ta yi ya nuna kokarin gwamnati na kare martabar makarantu na Najeriya.
Ana ganin idan aka ci gaba da irin haka, za a iya rage yawaitar makarantun bogi da kuma tabbatar da cewa duk wanda ya kammala karatu a Najeriya ya cancanci shaidar da ya samu.
Za a fara tallafawa iyayen daliban Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fara wani shiri na musamman domin mayar da yara makaranta.
Ma'aikatar ilimi ta bayyana cewa za ta fara ba iyaye mata tallafi na musamman domin karfafa su wajen mayar da yaransu makaranta.
Rahoton ya kara da cewa za a kara kudin tallafin karatu da ake ba 'yan Najeriya da ke karatu a manyan makarantun kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

