Yaki da Zaman Banza: Za a Koya wa Matasa Miliyan 1.5 Sana'o'i a Kano
- Hukumar fasahar sadarwa ta jihar Kano za ta haɗa kai da kungiyar KCI domin horas da matasa miliyan 1.5 sana'o'i
- Shirin zai gudana tsakanin 2025 zuwa 2027, inda za a koyar da matasa a matakai daban-daban na ilimin zamani
- An riga an fara aikin gwaji inda matasa 150,000 suka shiga, yayin da sama da 1,000 suka kammala horo a cibiyoyi na jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana sabon shirin horas da matasa miliyan 1.5 domin rage rashin aikin yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar.
Wannan yunƙuri na gudana ne ƙarƙashin Hukumar Cigaban Fasahar Sadarwa ta jihar (KASITDA) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar KCI.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa shugaban hukumar, Dr Bashir-Abdu Muzakkari, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da matasa da aka shirya a Zariya.

Kara karanta wannan
'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama
Dr Bashir-Abdu Muzakkari ya ce shirin ya haɗa da koyar da matasa a matakai daban-daban na ilimin zamani.
Dalilin horar da matasan jihar Kano
An ce manufar ita ce samar da dama ga matasa domin su zama ginshiƙai a ci gaban fasaha da tattalin arziki, tare da haɓaka kwarewar da za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi.
Dr. Muzakkari ya bayyana cewa shirin ya tsara kaiwa ga matasa miliyan 1.5 nan da shekarar 2027.
A cewarsa, a matsayin gwaji an riga an jawo matasa 150,000 cikin shirin, kuma 1,150 sun kammala karatu daga Cibiyar Kasuwanci ta jihar Kano da kuma Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Kura.
Ya ce gwamnati na shirin faɗaɗa tsarin zuwa manyan makarantu a jihar, domin kowane matashi ya samu damar shiga cikin wannan sabon tsari na ilimin zamani.
Karin bayani kan shirin HEAT a Kano
Shugaban ya bayyana cewa hukumar KASITDA ta ƙaddamar da wani shiri mai suna Hackathon HEAT wanda ya ƙunshi fannonin lafiya, ilimi, noma da sufuri.
Ya ce manufar ita ce shirya matasa domin samar da mafita ga matsalolin da ake fuskanta a waɗannan fannoni.
Ya kara da cewa gwamnati za ta tallafa wajen juyar da fasahohi da dabarun da matasan suka kawo domin warware matsalolin zuwa cikakkun kamfanoni.

Source: Facebook
Rawar da kungiyar KCI ke takawa a Kano
A nata jawabin, shugabar ƙungiyar KCI, Hajiya Aisha Muhammad, ta bayyana cewa ƙungiyar ta ɗauki nauyin buɗe ƙofofi ga matasa musamman a fannin fasahar zamani.
Kano Times ta wallafa cewa ta ce an kafa KCI ne da imanin cewa matsaloli na nan birjik a ko ina, amma damar warware su ba a ko’ina take ba.
Ta ce manufar su ita ce samar da kyakkyawar makoma ta hanyar taimaka wa matasa masu himma da ƙoƙari domin su koyi ilimi, kuma su kirkiri abubuwan da za su amfanar da al’umma.
Hajiya Aisha ta ce za su cigaba da haɗin gwiwa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen yada shirin zuwa sauran jihohi, domin rage matsalar rashin aikin yi da ƙarfafa tattali.
'Yan Sandan Kano sun kama barawon babur
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani gawurtaccen barawon babur.
Rahotanni sun bayyana cewa kama barawon ya jawo jami'an tsaro sun cafke mutane 10 da ake zargi da sayen kayan sata a jihar.
Binciken da jami'an tsaro suka gudanar ja jawo kama baburan da aka sace har guda bakwai tare da mayar da su ga masu su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

