Abubuwa 8 dake janyo rashin aikin yi a Najeriya

Abubuwa 8 dake janyo rashin aikin yi a Najeriya

Najeriya kasa mai tumunin arziki ida aka yi la'akari da abubuwan da take da su. Tana da ma'adanai da albarkatu na kasa, sai dai dole mu aminta cewa gwamnati kasar ta gaza tallafo wannan albarkatu da sanin muhammancin su wajen inganta tattalin arzikin kasar.

A sakamakon haka, al'ummar Najeriya su na fuskantar kalubale da kuma barazana mafi muni a ire-iren kasashen da suka ci gaba, wanda shine yawaitar rashin aikin yi.

Akwai dalilai da dama da suke janyo rashin aikin yi a Najeriya. Ci gaba da karanta wannan labarin na Legit.ng domin gano wadannan dalilai masu ciwo.

Matasa a fagen daga na neman abun yi
Matasa a fagen daga na neman abun yi

Shi dai abin da ake kira rashin aikin abu ne inda mafi yawan al'ummar kasa ba su da aikin yi wanda a turance ake cewa Unemployment. Hakan halin da ake ciki a Najeriya ya kaifar da wata mummunar matsala da take kasa da rashin aikin yi wanda ita kuma ake amfani da kalmar Underemployment a turance, wanda rashin sanin muhimmancin albarkatun kasar nan ya janyo mana.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya koma ofishin sa, ya na ganawa da shugabannin tsaro na kasa a yanzu

Za a yi adalci wajen yin batu na cewar akwai abubuwa fiye da 8 dake janyo wa kasar nan rashin aikin yi; sai wadannan sune jerin manyan dalilai wana suka danganci matsaloli na dokokin kasar nan.

1. Rashin samar da ingataccen ilimi

2. Rashin gaggawa wajen neman ilimin fasaha da sana'o'i

3. Cin hanci da rashawa

4. Kishin neman shiga siyasa a tsakanin matasa sakamakon irin maikon da suke hangowa.

5. Rashin amfanin basira ga matasa

6. Matsatsi na talauci

7. Son kai da ra'ayi wajen bayar da aikin yi a kasar nan, naka sai naka.

8. Hankoron aiki mai tsoka a tsakanin matasa, wai lallai sai anyi arziki cikin dare guda.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng