Arewa Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Gwamna kuma Sanata Ya Rasu a Abuja

Arewa Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Gwamna kuma Sanata Ya Rasu a Abuja

  • Najeriya ta yi babban rashi na tsohon gwamna kuma Sanata da ya yi mulkin soja a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya
  • Tsohon gwamnan soja na Plateau kuma Sanata da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana, ya rasu a Abuja ranar Juma’a
  • Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham, ya tabbatar da rasuwar, ya bayyana cewa marigayin ya bar mata da ’ya’ya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jihar Adamawa ta yi babban rashi bayan na rasuwar tsohon Sanatan a jihar da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Plateau, kuma Sanatan da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana.

Tsohon Sanata a Adamawa ya rasu a Abuja
Kanal Muhammad Mana ya mulki jihar Plateau kafin zama Sanata a Adamawa. Hoto: Usman Dahiru.
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Mana ya rasu ne bayan kwanaki biyu da aka sallame shi daga asibiti, inda ya sha fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Sarki mai martaba a Najeriya ya rasu yana mai shekaru 89

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a 22 ga watan Agustan 2025 a birnin Abuja.

Tarihin marigayi tsohon gwamna Muhammad Mana

An haifi Kanal Mana a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 1950 a jihar Adamawa inda ya riƙe muƙamai da dama kafin rasuwarsa.

Marigayin Mana ɗan asalin ƙaramar hukumar Maiha a Adamawa ne, kuma ya shugabanci Jihar Plateau daga Disamban 1993 zuwa Agustan 1996.

A zamanin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar, Mana ya zama kwamandan rundunar shugaban ƙasa a wancan lokaci.

Daga bisani, marigayin ya shiga siyasa inda ya tsaya takarar Sanatan Adamawa ta Arewa karkashin jam'iyyar PDP mai mulki a wancan lokaci.

Kanal Maha ya samu nasarar shiga majalisar dattawa a 2007 har zuwa 2011 kafin ya sha kaye a zaben fitar da gwani na kujerar Sanata wanda Umar Jibrilla Bindow ya kayar da shi.

Tsohon sanata a Adamawa ya yi bankwana da duniya
Taswirar jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaushe za a yi jana'izar marigayin a Abuja?

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Jakadan Najeriya ya rasu a lokacin da ba a yi tsammani ba

Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham, ya tabbatar da labarin, inda ya ce marigayin ya bar matansa da ’ya’ya.

Kwaccham ya bayyana cewa mutuwar marigayin babban rashi ne ga iyali da al’umma, musamman ganin irin rawar da ya taka wajen shugabanci.

Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 2:00 na rana Asabar 23 ga watan Agustan 2025 a Masallacin Juma’a na Ƙasa da ke Abuja.

Ana sa ran taron jama’a a yayin jana'izar duba da shaida mai kyau da aka yi wa marigayin da cewa yana da kyakkyawar alaka da mutane.

Mahaifin Gwamna ya riga mu gidan gaskiya

A baya, mun ba ku labarin cewa mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, Ahmed Momohsani Ododo ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar mahaifin gwamnan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada, ta yi addu'ar Allah ya gafarta masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.