Tsohon Gwamnan APC da ya sha kashi a 2019, ya dawo ya na neman takara a zaben 2023

Tsohon Gwamnan APC da ya sha kashi a 2019, ya dawo ya na neman takara a zaben 2023

  • Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya na rokon jama’a su sake ba shi dama ya karbi mulki a 2023
  • Sanata Jibrilla Bindow ya bayyana cewa idan ya zama Gwamna, za a ga cigaba a jihar Adamawa
  • A zaben 2019 ne Bindow ya sha kashi, ‘dan takarar da jam’iyyar PDP ta tsaida ya tika shi da kasa

Adamawa - Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Umar Jibrilla Bindow, ya bayyana burinsa na neman wani wa’adin a matsayin gwamna a karkashin APC.

The Cable ta rahoto Umar Jibrilla Bindow yana cewa zai so a ba shi wata damar domin ya karasa ragowar shekaru hudu da suka rage masa a gidan gwamnati.

Da yake zantawa da manema labarai a garin Yola, jihar Adamawa a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu 2022, Jibrilla Bindow ya nemi goyon bayan al’umma.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya maka Ministan shari’a gaban Alkali, ya na neman a biya shi N1.5bn

Bindow ya roki sauran masu neman kujerar gwamna a Adamawa a karkashin APC su kyale shi ya koma kan mulki domin ya kammala ayyukan da ya fara.

A cewar tsohon Sanatan, idan har ya sake zama gwamna, mutanen Adamawa za su ga cigaba a jihar. Jaridar Daily Post ta fitar da irin wannan rahoto a yau.

A ba ni dama a gani - Jibrilla Bindow

“Na yi abubuwa da-dama a lokacin da na ke gwamna, kuma ina da buri da yawa da na ke da shi ga jihar nan idan har aka yi dace aka sake zabe na 2023.”

- Jibrilla Bindow

Tsohon Gwamnan Adamawa
Bindow ya na neman tazarce a 2019 Hoto: www.legit.ng
Asali: UGC

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa muddin aka sake zaben shi a wani karon a shekarar badi, za a ga burin da yake da shi.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Dole a hada kai - Shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Adamawa, ya bukaci masu duk neman tikiti a zabe mai zuwa da hada-kai domin su yi nasara a zaben shekarar 2023.

Ibrahim Bilal ya na ganin sai kan ‘yan APC ya hadu sannan za a iya doke PDP a zaben gwamna da na shugaban kasa, domin gujewa abin yadda ya faru a 2019.

Sanata Umar Jibrilla Bindow wanda ya yi mulki tsakanin 2015 da 2019 ya sha kashi ne a hannun Ahmadu Umaru Fintiri a lokacin da ya nemi ya zarce a mulki.

APC da siyasar Katsina

Dazu kun ji cewa daga cikin wadanda za a gwabza da su wajen neman takarar kujerar gwamnan jihar Katsina a APC a 2023 akwai Arch. Ahmed Musa Dangiwa.

Dangiwa zai kara da su Mustapha Muhammad Inuwa, Ahmed Babba-Kaita, da Dikko Radda a jam’iyyar APC wajen gaje kujerar Gwamna Aminu Bello Masari.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Asali: Legit.ng

Online view pixel