Obasanjo Ya Kara Rubuta Littafi, Ya Fallasa Aika Aikar Alkalai a Najeriya
- Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce al'amarin shari'a a kasar nan ya tabarbare saboda tsabar cin hanci da rashawa
- Ya zargi cewa kotuna sun koma “kotun cin hanci” maimakon kotun adalci a sabon littafin da ya wallafa kan Najeriya a baya da kuma nan gaba
- Obasanjo ya ce siyasa a Najeriya tana dogaro ne da hukuncin alkalai fiye da kuri'ar jama’a, yana kuma zargin INEC da lalata tsarin zaɓe tun 2015
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda tsarin shari’a na Najeriya ya gama tabarbare wa.
Ya bayyana takaicin kan yadda ya ce yanzu alkalai sun fi karkata zuwa karbar cin hanci a maimakon tabbatar da adalci.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewar wannan na kunshe a cikin sabon littafin da rsohon Shugaban Kasar ya wallafa wanda ke magana kan Najeriya a da da kuma nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya magantu kan tsarin shari'a
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa tsarin shari’ar ƙasar nan ya samu matsala, musamman a mulkin dimokuraɗiyya na wannan ƙarni.
Obasanjo ya ce wannan koma-baya ya sanya jama’a sun daina aminta da shari’a saboda gaskiya yanzu mai kudi shi ne ke da gaskiya.

Source: Getty Images
Ya ƙara da cewa idan aka ci gaba da haka, za a maye gurbin adalci da tashin hankali, rikici da rudani, abin da ke da illa ga zaman lafiyar ƙasa.
A matsayin misali, Obasanjo ya bada labarin wata ziyara da ya kai jiha a Arewa bayan ya bar mulki, inda aka nuna masa manyan gidaje guda shida mallakar wani alƙali da ya tara kuɗi daga zama shugaban kotun zaɓe.
Zargin da Obasanjo kaya jefawa INEC
Obasanjo caccaki shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, yana cewa ya gurbata tsarin zaɓe tun daga 2015.
Ya ce hakan ya sa ‘yan siyasa da dama suka daina dogaro da ra’ayin jama’a, suna maida hankali ga hukuncin alkalai a kotunan sauraren ƙarar zaɓe, kotun daukaka ƙara da kuma kotun koli.
Obasanjo ya ce:
“Duk abin da jama’a suka zaɓa, sai dai abin da shugaban INEC ya rubuta ne zai tabbata."
“Abin da ya fi muni shi ne hukuncin alkalai – biyu cikin uku ko uku cikin biyar na iya soke ra’ayin miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a ta hanyar cin hanci.”
Obasanjo ya kuma danganta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da wannan matsala, yana zarginsa da yin yarjejeniya da alkalai a lokutan shari’ar zaɓensa.
Ya ce Buhari ya bai wa alkalai mukamai da fa’idodi domin samun goyon baya, lamarin da ya ƙara wargaza tsarin adalci.
Idan za a tuna dai Muhammadu Buhari ya rasu a watan Yuni, shekaru biyu bayan barin ofis.
Zargi ya fito kan zaben Obasanjo a 1999
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 1999, Cif Olu Falae, ya bayyana cewa shi ne ya ci zaɓe ba Olusegun Obasanjo ba.
Falae, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar AD-APP a wancan lokaci, ya yi ikirarin cewa shi ne ya samu mafi rinjayen ƙuri’u a zaɓen, sai dai aka sauya sakamakon.
Ya yi zargin cewa an shirya wannan dabara ne a matakin gwamnati domin tabbatar da cewa Obasanjo ne ya hau mulki, duk da cewa shi ya fi samun ƙuri’u a wuraren da zaɓe ya gudana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

