Najeriya Ta Samu Rancen $238m daga Japan, Minista Ya Lissafa Ayyukan da Za a Yi

Najeriya Ta Samu Rancen $238m daga Japan, Minista Ya Lissafa Ayyukan da Za a Yi

  • Gwamnatin tarayya ta samu rancen dala miliyan 238 daga Japan domin inganta tushen wuta da fadada makamashi a Najeriya
  • Wannan rancen zai taimaka wajen gina layukan wuta masu karfin 330kV, 132kV, da tashoshin wuta masu karfin 330/132/33kV
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Japan ta zama abokiyar hulɗa wajen rage gibin makamashi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Japan - Gwamnatin tarayya ta samu rancen kudi har dala miliyan 238 daga hukumar haɗin gwiwar kasa da kasa ta Japan (JICA) domin ƙarfafa tushen wutar lantarki na ƙasa.

Wannan ya biyo bayan tattaunawar da Shugaba Bola Tinubu da ministan makamashi, Adebayo Adelabu, suka jagoranta a taron Tokyo na kasa da kasa kan ci gaban Afrika karo na tara da aka gudanar a Yokohama, Japan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Japan ta amince za ta ba Najeriya rancen dala miliyan 238 don inganta tashar wutar lantarki
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zaune a dakin taron TICAD 9 da aka gudanar a Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Bola Tinubu ya halarci taron TICAD 9

Adebayo Adelabu, a sanarwar da ma'aikatar makamashi ta fitar ranar Juma'a, ya ce Shugaba Tinubu a wajen taron, ya bayyana nasarorin da Najeriya ta samu a tattaunawar TICAD 9, inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Najeriya ba ta halarci taron TICAD 9 don baje kolin kasuwanci kawai ba, bal, sai don kulla alaka da masu ruwa da tsaki na kasashe domin samar da ayyukan ci gaba da al'ummar kasarmu.
"Yanzu mun fara sauya wa matakin tsare-tsare zuwa aiwatarwa, daga matakin kulla yarjejeniya zuwa cika alkawuran da aka dauka."

- Adebayo Adelabu.

Najeriya ta samu rancen $238m daga Japan

Bashin da hukumar JICA za ta ba Najeriya na dala miliyan 238 ya samu amincewar majalisar zartarwa, inda ita ma Najeriya za ta zuba N19,083,192,805.30 don fadada aikin tushen wutar kasar.

Ayyukan da za a yi da kudin sun hada da kafa layin wuta mai karfin 330kV da ya kai tsayon kilomita 102.95, da kuma layin wuta mai karfin 132kV da ya kai tsayon kilomita 104.59.

Kara karanta wannan

Tinubu ya magantu daga Japan, ya fadi abin da ba a sani ba game da gwamnatinsa

Sauran sun hada da kafa kananun tashoshin wutar lantarki huɗu masu karfin 330/132/33kV, wasu kananun tashoshi biyu masu karfin 132/33kV, da kuma faɗaɗa wasu tashoshin layin rarraba wuta.

Adelabu ya ce tattaunawa da manyan kamfanonin wuta na Japan irin su Toshiba, Hitachi, da hukumar TDC ta Japan ta yi nisa domin buɗe damar samar da karin wutar lantarki a Najeriya.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce Japan ta kasance aminiyar amana ga Najeriya wajen ci gabanta a makamashi
Shugaba Bola Tinubu tare da shugabannin kasashen Afrika a taron TICAD 9, da aka gudanar a Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Kyakkyawar huldar Najeriya da Japan

TVC News ta rahoto Ministan makamashin yana cewa:

“Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne inganta tsarin rarraba wuta da wadatuwarta, da kuma rage asarar da ake yi. Da wannan rancen na dala miliyan 238 daga JICA za mu aza harsashin cimma haka.
"JICA ta riga ta tabbatar mana da cewa ita abokiyar hulda ce ta ama, kuma a shirye take ta taimaka wa Najeriya wajen bunkasa fannin makamashi da wadatuwar samar da wutar lantarki.
"Gudunmawar hukumar a fannin gine-gine, bincike, horo da kuma rancen kudi na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa bangaren makamashin Najeriya.”

Bugu da ƙari, Adelabu ya sake jaddada kudirin gwamnati na cike gibi a samar da makamashi, inda ya ce a halin yanzu kashi 55 zuwa 60 na 'yan Najeriya ne kawai ke da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dawo da shirin GEEP da mutane ke samun tallafin kudi da bashi a Najeriya

Bayan Japan, Tinubu zai ziyarci wasu kasashe

Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya bar Najeriya a ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 domin halartar wasu taruka a ƙasashe duniya.

Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ziyarci Japan da Brazil, inda zai halarci taro da ganawa da shugabanni.

A Japan ne aka ce Tinubu zai halarci taron taron Tokyo na kasa da kasa kan ci gaban Afrika karo na tara (TICAD 9) da aka shirya gudanarwa a Japan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com