'A Jira Mu," Gwamnatin Tinubu Za Ta Wallafa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci

'A Jira Mu," Gwamnatin Tinubu Za Ta Wallafa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci

  • Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai kan masu ɗaukar nauyin ta’addanci
  • Ya bayyana cewa jinkirin fallasa masu daukar nauyin ta’addanci ya samo asali daga batutuwan shari’a da alakar ƙasashen waje
  • Janar Musa ya ce NFIU, DSS da sauran hukumomin tsaro suna aiki tuƙuru wajen gano ’yan siyasar da ke da hannu a matsalar tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin tattara sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci tare da gurfanar da su.

Janar Musa ya ce jinkirin bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci ya samo asali ne daga sarkakiyar shari’a da kuma neman haɗin kan ƙasashen waje.

Hafsan tsaron Najeriya ya ce an kusa sakin sunayen masu daukar nauyin ta'addanci
Hafsan sojojin ƙasa, Olufemi Olatubosun Oluyede, ya gana da hafsan tsaro, Christopher Musa, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu a Abuja. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Babban hafsan tsaron ya bayyana hakan ne a daren Alhamis, 21 ga Agusta, 2025, a shirin 'Siyasa a yau' na gidan talabijin din Channels.

Kara karanta wannan

'Yakin ba na sojoji kadai ba ne,' Janar Buratai ya kawo dabarar murkushe 'yan ta'adda

Za a san masu daukar nauyin ta'addanci

Game da bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, Janar Christopher Musa ya ce:

“Muna kan tattara bayanai. An samu jinkirin ne saboda akwai batutuwan shari’a da kuma alaƙar da ta shafi ƙasashen waje.
"Wasu daga cikinsu suna aiko kuɗaɗen ne daga ƙasashen waje, ba za mu iya yi musu komai daga nan cikin gida ba, amma mun san su. Wasu kuma suna nan a cikin Najeriya.”

Ya ƙara da cewa akwai 'yan ta'addan da ke ba matasa babura, suna gudanar da ayyukansu, suna tura kuɗaɗe zuwa wasu asusun banki kuma, kuma hedikwatar tsaro na bibiyar shige da ficen kuɗaɗen domin gano tushensu.

Hedikwatar tsaro ta yaba wa NFIU

Janar Christopher Musa ya yaba wa hukumar NFIU bisa rawar da take takawa wajen gano yadda ake hada-hadar kuɗaɗe don ayyukan ta’addanci.

Hafsan tsaron ya ce:

“NFIU tana aiki sosai wajen bin sawun kuɗaɗen ta’addanci. Ban da bayanan leken asiri, ana bibiyar alaƙar kuɗaɗe sosai, kuma an riga an kama wasu.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

"Na tabbatar muku cewa ministan shari’a, Lateef Fagbemi, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, na aiki tuƙuru domin magance matsalar.”

Babban hafsan ya ƙara da cewa DSS, hukumar leken asiri ta ƙasa, da sauran hukumomin tsaro suna aiki don gano 'yan siyasar da ke ɗaukar nauyin ta'addanci.

Janar Christopher Musa ya ce hukumomin tsaro na iya kokarinsu don magance hare-haren 'yan ta'adda.
Hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa ya na magana yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin Katsina. Hoto: Mobile Media Crew
Source: Facebook

Ayyukan ta’addanci a Najeriya

Najeriya ta dade tana fama da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban, musamman Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Jihohin Arewa maso Yamma, musamman Zamfara, sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga, yayin da Arewa maso Gabas kuma ke fama da hare-haren Boko Haram.

Wadannan hare-hare sun yi sanadiyyar kisan dubunnan mutane tare da raba dubunnan daruruwan mutane da muhallansu.

An shawarci mutane su koyi dabarun fada

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya shawarci ‘yan Najeriya da su koyi dabarun faɗa domin kare kansu.

Janar Christopher Musa ya ce akwai bukatar mutane su koyi fasahohin faɗa irin su Karate, Taekwondo, Judo da koyon tuƙi, iyo da sauran su.

Hafsan tsaron ya ce ya kamata hukumar NYSC ta rika koyar da masu bautar kasa dabarun faɗa ba tare da makami ba domin tsira daga mugayen mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com