'Na Sha Tsangwama Sosai': Gwamna Ya Tuna yadda Ake Masa Ba'a ba Za a Zaɓi Zabiya ba
- Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana yadda aka yi masa ba’a yayin da yake kamfe na neman takarar gwamna
- Mai girma Gwamnan ya ce nuna masa wariya sosai saboda shi zabiya ne a yakin neman zaben 2023 a jihar Akwa Ibom
- Eno ya ce ya sha wahala tun yana yaro saboda halittasa, amma yau yana karrama masu irin wannan yanayi saboda nuna darajarsu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana yadda ya fuskanci izgili da wariya a jiharsa.
Gwamna Eno ya bayyana yadda ya sha wahala sosai kan cewa ba za a zabi zabiya a matsayin gwamna ba.

Source: UGC
A wani taro da aka gudanar a Uyo, gwamnan ya bayyana yadda aka yi amfani da yanayinsa wajen siyasa domin bata masa suna, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
An dauki gwamna 1 a Najeriya, an ba shi lambar yabo ta 'Zabin Jama'a' a kasar Faransa
Yadda ake tsangwanar zabiya a wasu wurare
Zabiya cuta ce ta gado wadda ke haifar da rashin sinadarin 'melanin' a fata, gashi da ido, inda hakan ke haddasa matsalolin gani mai tsanani.
Hakan ya sanya wasu daga cikinsu ke fargabar shiga cikin jama'a saboda yadda wasu ke tsangwamarsu duba da cewa ba su suka halicci kansu a haka ba.
Mutane da dama suna yi wa masu halittar zabiya ba'a wanda ke jawo nuna wariyar launin fata da kuma halitta.
Gwamna ya karrama zabiya a Akwa Ibom
Gwamna Eno wanda aka yi masa ba'a a baya ganin cewa shi zabiya ne ya bayyana irin kimar da masu irin halittar suke da ita.
Ya kuma karrama yara masu irin wannan hali, yana cewa:
“Mutane da ake kira zabiya sun kasance na musamman kuma suna da gwamna na musamman."
“Lokacin da muka fara kamfen, wasu sun ce ba sa son gwamna zabiya sai matata ta ce, kai 'yaro ne na musamman'.”

Source: Facebook
Gwamna ya koka kan nunawa zabiya wariya
Eno ya bayyana cewa ana ware zabiya sau da dama kuma ana musu izgili, har ma ba a ba su dama a bainar jama’a wanda haka tauye hakkinsu.
“Ina tunawa, ba sa ba mu dama a baya, suna kiranmu da sunaye, suna hana mu bayyana a fili. Amma yau Allah ya fito da mu.”
- Cewar Gwamna Eno
Ya ce saboda haka duk inda ya ga mai irin wannan yanayi sai ya mutunta shi, ya kuma nuna cewa su ma suna da daraja, Tribune ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana yadda ya girma a matsayin zabiya, inda ya ce:
“Na fuskanci izgili, cin zarafi da wariya, amma yau ina alfahari.”
Ya ce shi ya sa duk lokacin da ya hadu da mai wannan halitta, sai ya karrama shi domin tabbatar da darajarsa.
Gwamna Eno ya faɗi dalilinsa na komawa APC
Kun ji cewa Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya fadi dalilansa na komawa jam'iyyar APC inda ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu.
Eno ya ce cire tallafin fetur ya sa gwamnoni suka fi samun kudi, inda ya bayyana alherin da Akwa Ibom ke samu a sakamakon hakan.
Ya ce wannan sauyin siyasa hadaya ce ga Tinubu a ranar Sallah, yana kuma tabbatar da goyon bayansa ga ayyukansa na musamman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

