Hotunan Sauyawar Yarinyar Da Aka Haifa A Matsayin Zabiya Shekaru Bayan Mahaifinta Ya Gujeta

Hotunan Sauyawar Yarinyar Da Aka Haifa A Matsayin Zabiya Shekaru Bayan Mahaifinta Ya Gujeta

  • Wata uwa ta bayar da labarin diyarta wacce ta kasance zabiya amma sai mahaifinta ya yi watsi da ita bayan haihuwarta
  • Uwar mai suna Nshai ta wallafa wani bidiyo da ke nuna sauyawar kyakkyawar diyar tata shekaru bayan haihuwarta
  • Yayin da take wallafa bidiyon, ta bayyana cewa mutumin da ya yi watsi da diyarta a yanzu ya dawo yana so a kira shi da ubanta

Wata uwa da ta cika da alfahari ta nuna yadda kyakkyawar diyarta da aka haifa zabiya ta sauya ta kara kyau.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Nshai ta ce mahaifin diyar tata ya yi watsi da su lokacin da aka haifi yarinyar. Baya kaunarta saboda an haifeta zabiya.

Zabiya
Hotunan Sauyawar Yarinyar Da Aka Haifa A Matsayin Zabiya Shekaru Bayan Mahaifinta Ya Gujeta Hoto: @nshaimahvaldez
Asali: UGC

Sai dai kuma, shekaru bayan nan, yanzu yana roko don ya dawo cikin rayuwarta kuma a matsayin mahaifinta.

Kara karanta wannan

Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

Da take wallafa bidiyon sauyawar diyar tata tun daga lokacin da aka haifeta har zuwa yau, Nshai ta rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya watsar da mu sanoda ba nice irin diyar da yake so a rayuwarsa ba. yanzu na zama kyakkyawar diya yana rokon na dawo cikin rayuwarsa sannan na kirasa mahaifina.”

Jama’a sun yi martani

@hibahnajj004 ta ce:

“Kuma bashi da sauran daman a dawowa rayuwar diyarmu.”

@jbella76 ya yi martani:

"Waaaaaoooo. Tana da kyau matuka….Wayyo Allah.”

@sega588 ta ce:

“Kin sanya murmushi a fuskata yanzu tun safe nake kuka, ta hadu sosai.”

@musiitwagift ta yi martani:

“Na yi kewar Shaimah lokacin da take karama. Ta kasance katuwa. Masha Allah."

Kalli bidiyon a kasa:

Ta Musamman Ce: Bidiyon Yarinya Mai Wani Nau'in Tabon Haihuwa Ya Bar Jama'a Baki Bude

A wani labarin, wata karamar yarinya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya saboda kyawun halitta irin nata, tana dauke da wani tabon haihuwa mai matukar haske a goshinta.

Kara karanta wannan

Zan Saketa Bayan Wata 2 Sai Muyi Aurenmu: Matashi Ya Sanar Da Budurwarsa Labarin Aurensa Da Wata Daban

Allah ya yiwa kyakkyawar yarinyar wata baiwa da ba a saba gani ba a fuskanta wanda ya sace zukatan jama’a inda suka jinjina mata.

A bidiyoyi da dama da mahaifiyarta mai suna @tasharuth00 ta wallafa a TikTok, kyakkyawar yarinyar ta baje wannan tabo nata yayin da take rera waka mai dadin sauraro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel