Zaben 2027: An Gano Yadda ake Amfani da Siyasa wajen Zafafa Hare Hare a Najeriya

Zaben 2027: An Gano Yadda ake Amfani da Siyasa wajen Zafafa Hare Hare a Najeriya

  • Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya ce yawaitar kashe-kashen da ake samu yanzu a Najeriya ba za a raba shi da shirye-shiryen siyasa gabanin zaben 2027 ba
  • Ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa na rura wutar rikice-rikice don su bata sunan gwamnati, tare da amfani da ta’addanci da ‘yan bindiga wajen kawo cikas ga zaman lafiya
  • Janar Musa ya nuna cewa ana taimakawa ta'addanci da kudi a cikin gida da kasashen waje, inda ya nemi kafa kotuna na musamman don gudanar da shari’a ga 'yan ta'adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce tashin hankali da ya ƙaru a sassan ƙasar a ‘yan watannin nan ba ya rasa nasaba da shirye-shiryen zaɓen 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano sabuwar hanyar da ake daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Najeriya na fuskantar hare-haren ta’addanci a Arewa maso Gabas da kuma ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, yayin da jihohin Benue da Filato suka ci gaba da kasancewa cibiyoyin kashe-kashe.

Hafusn tsaron Najeriya, Janar Musa
Hafusn tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Janar Musa ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin da ta gabata, akalla mutane 34 suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a masallaci da ke Unguwar Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Me ya jawo karin hare hare a Najeriya?

Yayin da yake bayani, Janar Musa ya ce yadda rashin tsaro ya ƙaru idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata ya nuna akwai hannun siyasa a ciki.

Ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na amfani da rikici wajen bata suna da kuma nuna cewa gwamnati ta gaza.

A cewarsa:

“Yan bindiga da ‘yan ta’adda suna aiki tare domin samun kuɗi da tayar da hankali. Amma akwai kuma bangaren siyasa.
"Wasu mutane ba sa son zaman lafiya, domin idan an samu zaman lafiya, ana ganin gwamnati na yin nasara. Idan babu zaman lafiya, ana ganin ta gaza.”

Kara karanta wannan

Adamawa: An kama matar da ke sace yara daga Arewa zuwa Kudu ta sayar da su

Ya kara da cewa abin mamaki ne yadda mutane ke kashe jama’ar da suke neman mulka, yana tambaya:

“Me kuke samu daga kashe mutanen da kuke son ku shugabanta?”
Hafsun tsaro, Christopher Musa a kasar Kamaru
Hafsun tsaro, Christopher Musa a kasar Kamaru. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Janar Musa ya ce ana tallafawa 'yan ta'adda

Punch ta rahoto cewa Janar Musa ya bayyana cewa ta’addanci a Najeriya na cigaba ne bisa tallafin kuɗi daga ciki da wajen ƙasar.

Ya ce ana ci gaba da binciken waɗanda ke daukar nauyin ta’addanci tare da hadin gwiwar Babban Lauyan Ƙasa, Hukumar NFIU, DSS da NIA.

Ya bayyana cewa akwai hannun ƙasashen waje da ke taimaka wa ‘yan ta’adda, inda ya tabbatar da cewa ana bin diddigin lamarin.

Janar Musa ya yi misali da wadanda suke da hannu a harin Owo, inda ya ce an riga an kama su kuma suna fuskantar shari’a.

An kama makamai a jihar Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama tarin harsashi a iyakar jihohin Yobe da Gombe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama harsashin ne a wata mota a karamar hukumar Nafada da ke jihar Gombe.

Binciken sojojin Najeriya ya nuna cewa matukin motar ya fito daga jihar Borno ne da nufin isar da makaman zuwa jihar Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng