Mutane Sun Kama Wata Baiwar Allah Bisa Kuskuren Zargi, Sun Kashe Ta a tsakiyar Kasuwa

Mutane Sun Kama Wata Baiwar Allah Bisa Kuskuren Zargi, Sun Kashe Ta a tsakiyar Kasuwa

  • Mutane sun yi kuskuren kashe wata mata marainiya bisa zargin tana da alaka da masu garkuwa da mutane a Ilorin, babban birnin jihar Kwara
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da matar ta shiga unguwa tana yawo, mutane suka far mata babu gaira-babu dalili
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kwara ta yi Allah wadai da kisan matar, wacce daga bisani aka gano marainiya ce da ke yawo kwararo-kwararo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara - Wata wata da aka yi kuskuren zargin tana da hannu a garkuwa da mutane ta rasa ranta a hannun fusatattun jama’a a kasuwar Ipata da ke Ilorin, jihar Kwara.

Sai dai bayan mutane sun hallaka matar ne aka gano cewa ba ta da hannu a ayyukan yan bindiga ko masu garkuwa da mutane, kuma abin takaicin marainiya ce.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta

Jihar Kwara.
Hoton taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton Tribune Nigeria ya tattaro cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar ranar Laraba, lokacin da aka ga matar tana yawo a cikin Unguwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe wata mata a kasuwar Ilorin

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, ya bayyana shi a matsayin abin takaici.

“Rundunar yan sanda ta samu labarin mummunan lamari da ya faru a ranar Laraba da misalin ƙarfe 9:00 na safe a yankin kasuwar Ipata, Ilorin.
"Bayanin da muka samu ya nuna cewa an ga wata mace da ake kyautata zaton marainiya ce tana yawo a unguwar, wasu mutane da ba su da sahihin bayani sun yi zaton ‘yar garkuwa ce.
"Daga nan ne suka mata taron dangi, suka yi mata mummunar illa. 'Yan sanda sun kai dauki, suka kwace matar daga hannun jama'a suka garzaya da ita asibiti.

Kara karanta wannan

Adamawa: An kama matar da ke sace yara daga Arewa zuwa Kudu ta sayar da su

"Abin bakin ciki, likita ya tabbatar da mutuwarta sakamakon munanan raunukan da ta samu. An ajiye gawarta a dakin ajiye gawarwaki, mun fara bincike na sirri."

- In ji Toun Ejire-Adeyemi.

Dakarun yan sandan Najeriya.
Hotun yan sanda a motar sintiri Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda ta yi Allah wadai da kisan matar

Rundunar ‘yan sanda ta yi Allah wadai da wannan mummunan aiki na daukar doka a hannu, tana mai cewa hakan na ƙasƙantar da doka tare da jefa rayukan mutane marasa laifi cikin haɗari.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kwara, CP Adekimi Ojo, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda, tare da kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi caji ofis mafi kusa.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa yan sanda haɗin kai wajen kare doka, oda da adalci tare da gujewa duk wani nau’in tashin hankali, rahoton Guardian.

An kama masu garkuwa da mutane a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ’yan sanda ta Abuja ta tabbatar da kama wasu manyan barayi, tare da kwato makamai da kudin fansa daga hanunsu.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta dakume manyan barayi da jagoran 'yan ta'adda a Abuja

Rundunar ta bayyana cewa wadannan bata garin mutane sun addabi mazauna birnin tarayya da wasu sassan jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa wannan nasara ta biyo bayan rahotannin garkuwa da dama a yankunan Karu, Guzape, Karshi, Kurudu, Jikwoyi da Apo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262