Bill Gates: Attajiri Ya Ware Gwamna 1 a Arewa, Ya Faɗi Ɓangaren da Ya Yi Fice a Najeriya

Bill Gates: Attajiri Ya Ware Gwamna 1 a Arewa, Ya Faɗi Ɓangaren da Ya Yi Fice a Najeriya

  • Attajirin nan, Bill Gates ya ware gwamnatin jihar Gombe inda ya yaba mata na musamman kan kawo sauyi a bangaren lafiya
  • Bill Gates ya yi yabon ne bisa gyaran fannin lafiya, inda ya ce tsarin jihar abin koyi ne kuma yana kawo sakamako mai gamsarwa
  • Mai kudin ya bayyana hakan ne a wata wasika, yana jinjina ga tsarin gudanarwa, hadin kai da kuma kirkire-kirkire

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Shahararren attajiri kuma shugaban Gidauniyar Gates, Bill Gates, ya yaba wa gwamnatin jihar Gombe.

Attajirin ya yaba Gwamnan Gombe ne bisa manyan gyare-gyaren a bangaren lafiyar da ta aiwatar, yana kiran tsarin abin koyi.

Bill Gates ya yabawa Gwamna Inuwa
Attajiri Bill Gates ya ce zai ci gaba da sa ido kan jihar Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli, Bill Gates.
Source: Facebook

Bill Gates ya yabawa gwamnatin jihar Gombe

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya tabbatar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan korafe korafe, Tinubu ya dauki alƙawari bayan kisan masallata a Katsina

Misilli ya ce Bill Gates ya fadi haka ne cikin wasikar da ya tura ga gwamnatin jihar ta hannun hukumar 'GoHealth da Human Capital Managers Nigeria Limited'.

Bill Gates ya ce yana alfahari da yadda gwamnatin jihar ke magance matsaloli domin samun sakamako mai kyau.

Ya jaddada cewa mayar da hankali kan shigar da masu ruwa da tsaki da kuma tsarin shugabanci na dabaru shi ne ginshikin nasarar da aka samu.

Bangarorin da Gates ya ce an samu sauyi

Gates ya bayyana sauyin da aka samu a harkar lafiya a Gombe a matsayin abin koyi, sakamakon jagoranci mai hangen nesa da tsare-tsaren fasaha.

Ɗaya daga cikin kirkire-kirkiren da ya jinjina shi ne manhaja ta cikin gida wadda ke inganta gudanarwa da rarraba albarkatu.

Ya bayyana wannan tsarin a matsayin kyakkyawan misali na shirin gwamnati da ke amfani da bayanai kai tsaye wajen tsara ayyukan kiwon lafiya da albarkatun jihar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Wike ya fadi matsayarsa kan masu marawa Tinubu baya

Gates ya nuna farin ciki da yadda tawagar jihar ta yi bayani dalla-dalla a taron, inda ya yaba da jajircewar shugabanni da kwararrun jami’an gwamnati.

Attajiri Bill Gates ya kwarara yabo ga Inuwa
Gwamna Inuwa Yahaya yayin taro a gidan gwamnatin Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

Abin da Gates ya ce zai yi nan gaba

Attajirin ya ce zai ci gaba da sa ido kan cigaban da ake samu a jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas a Najeriya.

Sanarwar ta ce wannan yabo daga fitaccen mai fafutukar kiwon lafiya ya tabbatar da jajircewar jihar wajen kawo ci gaba da sabbin tsare-tsare.

Ismaila ya bayyana cewa gwamna kullum yana jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta lafiyar jama’a ta hanyar gaskiya, inganci da samar da daidaitaccen kulawa.

Ya kuma ce jihar na da cikakken shiri na ci gaba da fadada nasarorin da aka samu a bangaren lafiya don ciyar da jama’a gaba cikin walwala.

Legit Hausa ta tattauna da yan Gombe

Wani ma'aikacin lafiya a Gombe, Muhammad Sunusi ya ce a gaskiya akwai gine-gine kam amma babu komai a ciki.

Ya ce:

"Kmar mu da ke aiki a cibiyoyin lafiya mataki farko, ginin ma da hadin guiwar Bankin Duniya da wasu hukumomi ake daukar nauyi."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bullo da shirin afuwa ga 'yan daba, ta fadi wadanda za su amfana

Sai dai wani ma'aikacin lafiya a gwamnatin jiha, Musa Ibrahim ya ce a gaskiya Gombe sai son barka saboda an samu sauyi sosai a mulkin Gwamna Inuwa.

Gwamna Inuwa ya magantu kan zaben 2027

A baya, kun ji cewa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ce addu’a ta fi komai yayin da ake ta rade-radin wanda zai gaje shi a 2027 a Gombe.

Ya ce bai kamata a gaggauta batun magaji ba, domin Allah ne ke ba da shugabanci, amma yana fatan samun wanda zai gaje shi.

Dangane da dokar hana babura da dare, Inuwa ya ce gwamnati za ta samar da bas-bas don saukaka sufuri daga ƙarfe 7:00 na dare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.