Sheikh Daurawa Ya Jero Abubuwa 7 da za Su Karawa Mace Daraja

Sheikh Daurawa Ya Jero Abubuwa 7 da za Su Karawa Mace Daraja

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana abubuwa bakwai da suka wajaba mace ta kiyaye domin ta samu daraja a Musulunci
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa malamin ya yi wannan nasiha ne a yayin wa’azi a Jami’ar North West da ke jihar Kano
  • Legit Hausa ta rahoto cewa Daurawa ya ce kiyaye wadannan dokoki zai kare mutuncin mace a matsayin ta na ‘ya, uwa da kuma mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya jaddada muhimmancin kiyaye dokokin Musulunci da suka shafi martabar mace.

Ya bayyana cewa addinin Musulunci ya ba mace matsayi na musamman wanda ya kamata ta kula da shi ta hanyar kiyaye tsari da ladubban da aka shimfida.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki

Shugaban Hukumar Hisba ta Kano, Sheikh Daurawa.
Shugaban Hukumar Hisba ta Kano, Sheikh Daurawa. Hoto: Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Abubuwan da ake so mace ta kiyaye - Daurawa

A bidiyon wa'azin da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya lissafa wasu abubuwa bakwai da ya kamata mace ta yi domin samun daraja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya bayyana wannan ne a yayin wani wa’azi da ya gabatar a Jami’ar North West da ke jihar Kano.

1. Rufe tsiraici na da muhimmanci

Sheikh Daurawa ya ce wajibi ne mace ta rufe duk wani abu da ya shafi tsiraici a jikinta idan za ta fita daga gida.

Wannan shi ne ginshiƙi na farko da zai kare mutuncin mace, domin bayyana tsiraici na rage martabarta a idon al’umma da kuma addini.

2. Rufe kwalliya wajibi ne

Malamin ya bayyana muhimmancin rufe kwalliya idan mace za ta fita waje, saboda addini bai yarda mace ta je wajen jama’a da kwalliyar da za ta jawo hankalin maza ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta yi wa tubabbun 'yan daba auren gata a Kano

Hakan yana da muhimmanci ne matuka kasancewar mata sun saba yin kwalliya sosai idan za su fita wani waje.

Sheikh Daurawa yayin da ya ke wani wa'azi a jihar Gombe
Sheikh Daurawa yayin da ya ke wani wa'azi a jihar Gombe. Hoto: Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

3. Ba a so mace ta fesa turare

Sheikh Daurawa ya ja hankalin mata game da yin amfani da turaren da zai cika wuri da kamshi idan suna cikin jama’a.

Ya ce hakan ba daidai ba ne, sai dai mace za ta iya amfani da turaren da zai hana jikinta tsami, ba wanda ake amfani da shi domin kamshi kawai ba.

4. Hani kan rangada murya a waje

Malamin ya yi gargadi ga mata da kada su rika rage murya ko rangwada ta idan suna magana da maza da ba muharramansu ba.

Sheikh Daurawa ya fadi haka ne saboda rangwada murya zai iya kawo fitina kuma yana rage martabar mace a idon al’umma.

5. Kada ta kebanta da namiji

Shehin ya ce bai halatta mace ta kasance a wuri ita da namiji su kadai ba, domin hakan na iya jawo abin da bai dace ba.

Wannan mataki yana daga cikin hanyoyin da Musulunci ya shimfida domin kare martabar mace a idon duniya.

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

6. Rashin cudanya da maza

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce bai kamata mace ta kasance tana cudanya da maza a wajen aiki ko taro ba.

Ya bayyana cewa addini ya tsara a samu tazara tsakanin maza da mata a irin wadannan wurare domin kauce wa fitina da kuma kare mutunci.

7. Kada ta gaisa da namiji ko ya taba ta

A karshe, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa bai halatta mace ta gaisa da namiji da hannu ba ko kuma ta bari ya taba jikinta.

Sheikh Daurawa ya jaddada cewa kiyaye wadannan matakai bakwai zai taimaka wajen kare darajar mace a Musulunci.

Ya yi addu’a ga daliban jami’ar da Allah ya basu nasara a dukkan al’amuransu tare da kasancewa masu kiyaye mutuncin su a duk inda suka kasance.

Hukuncin sallah da tufafi mai hoto

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Jabir Sani Mai Hula ya yi bayani ga musulmai kan hukuncin sallah da tufafi mai dauke da hoto.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Hadimar gwamna ta rasu kwatsam, gwamnati ta tura sako ga iyalanta

Malamin ya bayyana cewa ba ya halatta ga musulmi ya yi sallah da riga mai dauke da hoton 'yan siyasa da sauransu ba.

Sai dai duk da bayanin da ya yi, Dr Mai Hula ya bayyana cewa ba dole ne sai an sake sallar da aka riga aka yi da irin tufafin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng