Matsayin mata a addinin Musulunci

Matsayin mata a addinin Musulunci

Mace itace mutun na farko da ta fara karban addinin musulunci wato Uwargidan mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a kareshi (Nana Khadija bint Khuwalid).

Ta kasance babban mai fatauci, ta kuma yi ma addinin musulunci hidima da jikinta da kuma dukiyarta.

A lokacin da addinin musulunci ya zo, ya dakatar da duk wani zalunci da ake yi wa mata, ya mayar musu da 'yancinsu, ya kuma ba su rabo daga cikin gado.

Matsayin mata a addinin Musulunci

Allah ya bayyana cewa ita mace abokiyar rayuwar namiji ce, ya kuma mutunta ta a cikin mutane.

Har ila yau kamar yadda suke tarayya da maza wajen samun ladan aikata aiki nagari, haka kuma suke samun zunubi wajen aikata mummunan aiki.

Kamar yadda yazo a fadin Allah (S.W.T) yana cewa: "Wanda ya aikata aiki nagari, namiji ne ko mace alhali yana mumini lallai za mu raya shi rayuwa mai dadi, kuma za mu saka musu ladansu da mafi kyawun abin da suka aikata."

Wani gata da musulunci ya yi wa mace shi ne, haramta mayar da ita kayan gado da ya yi, sannan ya tabbatar da cewa a ba ta gado idan miji ko kuma wanda gadonsa ya wajaba a gare ta ya mutu.

Bayan haka musulunci ya duba alfarmar mace ya martabar ta, ya darajar ta sannan kuma ya daukaka ta ya zaba mata yin hijabi (sutura) wadda za ta rufe jikinta domin kare mutuncinta.

Matsayin mata a addinin Musulunci

Allah (S.W.T) a cikin hikimominsa da ba za sa, ya halicci halittu guda biyu wato mace da namiji ya kuma sanya kowanne ya zama abokin rayuwar dayan, ko da rayuwar dayan za ta yiwu ba tare da dayan ba.

To lallai dayan ba zai ji dadin rayuwar ba, kuma al'umma ba za ta yadu ba, saboda kasantuwar rashin dayan.

Ubangiji bai bar mutum haka ba sai da ya ajiye sharadi akan cewa namiji ba zai kusanci mace ba har sai ya cika wasu sharadu wato ya biya sadakin ta, shaidu, sannan ta halatta a gare shi.

Babu shakka zuwan addinin musulunci ya sauya duk wani kuncin rayuwa da mata ke fuskanta a baya kafin zuwan sa. Sannan ya daukaka martabar ta da suturtata har ta zamo abun takawa a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel