Malamin Addini Ya Yi Hasashe kan Tazarcen Tinubu, Ya Fadi Sharadin da Zai Sa Ya Sha Kaye
- Fasto Joel Atuma ya bayyana sabon hasashensa game da makomar siyasar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- FastoAtuma, wanda ya shahara wajen yin irin wadannan maganganun, ya sake yin wani hasashe yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa
- Yayin da jam’iyyun adawa ke tsara dabaru domin kayar da Tinubu, malamin addinin ya bayyana ra’ayinsa kan yiwuwar Tinubu ya sake dawowa mulki a 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Umuahia, jihar Abia - Fasto Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Malamin addinin ya ce kafin karshen shekarar 2026, Shugaba Bola Tinubu zai iya sanin ko ya yi nasara ko kuma bai yi ba.

Source: Facebook
Fasto Joel Atuma ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani bidiyo da aka wallafa a tashar YouTube dinsa.

Kara karanta wannan
"Kan mage ya waye": Jam'iyyar PDP ta kada hantar APC, ta fadi abin da zai faru a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya ce Tinubu ya fi karfin 'yan adawa
Malamin addinin ya yi ikirarin cewa jam’iyyun siyasa ba za su iya hana Tinubu tazarce ba, amma zai iya faduwa ne a kan sharadi ɗaya.
Bidiyon ya samu fiye da masu kallo 3,000.
"Zaɓen Najeriya a kalanda za a yi shi ne a 2027, amma a duniyar rauhanai, zaɓen za a yi shi ne a 2026. Kafin karshen 2026, shugaban kasa zai riga ya san ko ya yi nasara ko bai yi ba."
- Fasto Joel Atuma
Ya kara da cewa akwai wasu manyan abubuwa da za su tantance nasararsa, amma ba su da alaka da kuri’un zaɓe.
Wane sharadi zai hana Tinubu tazarce?
"Na gaya muku cewa shugaban Najeriya zai kai wani matsayi da babu wanda zai iya yin takara da shi."
"Kuma na ce zai tarwatsa jam’iyyun adawa, sannan ya tabbatar babu wata bukatar adawa, babu kuma amfanin yin zaɓe."
"Idan hakan ta faru, Allah zai bar shi ya kai wannan matsayin da yake ganin shi ba zai iya taɓuwa ba.”
"Zai fadi zaɓe ne a kan sharadi ɗaya. Ina so ku saurare ni, jam’iyyun siyasa ba za su iya hana shi ba, amma shugaban Najeriya zai fadi zaɓe idan wannan sharadin ya cika."
"Idan hakan ya faru a badi, duk wanda ’yan Najeriya suka zaɓa ba, ba zai ci nasara ba. Ku rubuta maganata, na ce ko dukkan 'yan Najeriya sun zaɓe shi, ba zai sake zama a kujerar nan ba. Wannan ne lokacin da Allah zai fara bayyana girmansa."
"A lokacin ne za ku fahimci abin da ake kira ‘ikon shawarwarin Allah kan kaddarar Najeriya’. Idan hakan ya faru a badi, to ba zai ci nasara a 2027 ba. Kuma akwai wata kalma da ta shafi wannan. Zan dawo in gaya muku wannan kalmar.”
- Fasto Joel Atuma

Source: Facebook
Tinubu ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana shirinsa kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta magance tushen matsalar domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Ya kuma yaba da irin jajircewa da sadaukarwar da dakarun sojoji suke yi wajen ganin ceqa sun kawo karshen ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
