Rundunar 'Yan Sanda Ta Dakume Manyan Barayi da Jagoran 'Yan Ta'adda a Abuja

Rundunar 'Yan Sanda Ta Dakume Manyan Barayi da Jagoran 'Yan Ta'adda a Abuja

  • Rundunar ’yan sanda ta Abuja ta tabbatar da kama wasu manyan barayi, tare da kwato makamai masu ƙarfi da kuɗin fansa daga hannunsu
  • An kama wani matashi mai suna Masud Abdullahi, wanda ya amsa laifin satar bayin Allah da dama a yankunan Asokoro, Guzape, Karu, Kurudu da Apo
  • Jami'an sun yi nasarar cafke mutane biyu daga cikin 'yan ta'addan da motarsu ta yi hadari bayan sun karbo kudin fansa a hanya Abuja zuwa Nasarawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar ’yan sandan Abuja ta samu nasarar cafke wasu shahararrun masu garkuwa da mutane da kuma 'yan fashi da makami.

Rundunar ta bayyana cewa wadannan bata garin mutane sun addabi mazauna birnin tarayya da wasu sassan jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Adamawa: An kama matar da ke sace yara daga Arewa zuwa Kudu ta sayar da su

Yan sanda sun kama 'yan ta'adda
Wasu daga cikin yan sandan Najeriya (H), Sufeton 'yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun Hoto: Nigerian Police Force
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa an kuma kwato mugayen makama, harsashi da wani kaso na kuɗin fansa da aka karɓa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan ta'adda sun addabi mazauna Abuja

Rahotanni sun nuna cewa wannan nasara ta biyo bayan rahotannin garkuwa da dama a yankunan Karu, Guzape, Karshi, Kurudu, Jikwoyi da Apo.

Cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da lauya, Barista Henry Chichi, wanda aka sace daga gidansa a De Villa Estate, Karu, ranar 16 ga watan Agusta, 2025 inda aka buƙaci fansar N100m a tayin farko.

An kama 'yan ta'adda a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daga bisani 'yan ta'addan su ka rage kudin da su ka nema a matsayin fansa zuwa N25m idan yana bukatar ya tsira da rai.

'Yan sanda sun kama 'yan ta'adda

Bayan samun bayanan sirri, 'yan sandan Abuja da hadin gwiwar na Nasarawa sun bi sawun ’yan ta’addan bayan sun gamu da hatsari a kan hanyar Abuja–Nasarawa.

Kara karanta wannan

Dilolin kwaya 2 sun gamu da hukumar NDLEA, kotu ta yanke masu shekaru 10 a kurkuku

Jami'an sun yi nasarar cafke ɗaya daga cikinsu mai suna Mohammed Tahir daga Jos a motar Opel Vectra da suke amfani da ita.

Daga cikin abubuwan da aka samu a tare da shi akwai kuɗi har N6.9m, bindiga AK-47, bindiga G3 da wasu makamai masu hadarin gaske.

A ranar 20 ga Agusta, 2025 an kuma kama wani matashi mai shekara 20, Masud Abdullahi wanda aka fi sani da “Small” a dajin Gurkwu, jihar Nasarawa.

An same shi da N537,000 da waya, ya kuma amsa cewa shi ne shugaban masu garkuwa da mutanen da aka bi sawunsu.

Ya ce ya jagoranci garkuwa da dama a Asokoro, Guzape, Jikwoyi, Kurudu, Karu da Apo. Ya kuma ce ya samu rabon N1m daga garkuwa da Mary Apeh, bayan sun harbi mijinta.

An bukaci a kashe dan ta'adda, Turji

A baya, kun samu labarin cewa tsohon mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa bai dace gwamnati ta amince da tayin sulhun Bello Turji ba.

Wannan martani na Bashir ya biyo bayan rahotannin da su ka nuna cewa Turji ya nuna shirinsa na ajiye makamai tare da yaransa idan aka ba su damar zaman lafiya.

Bashir Ahmad ya jaddada cewa wannan furuci na Turji alama ce kawai da ke nuna cewa ya fara fahimtar ƙarshen rayuwar ta’addancinsa ya kusa zuwa, yana neman mafita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng