Gwamnati Ta Rufe Shafukan 'Yan Najeriya Miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

Gwamnati Ta Rufe Shafukan 'Yan Najeriya Miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

  • Gwamnatin tarayya ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13,597,057 a dandalin TikTok, Facebook, Instagram da kuma X
  • Rahoton bin Dokar CoP ta 2024 ya nuna cewa ana amfani da wadannan shafukan wajen wallafa abubuwan da basu dace ba
  • NITDA ta ce goge shafukan zai ƙara tsaron yanar gizo, kuma za ta ci gaba da wayar da kan masu amfani da soshiyal midiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta rufe akalla shafukan sada zumunta na 'yan Najeriya 13,597,057 saboda yada bayanan da ba su dace ba da kuma karya ƙa’idar amfani da soshiyal midiya.

An ruwaito cewa sama da 'yan Najeriya miliyan 13 sun rasa shafukansu na TikTok, Facebook, Instagram da X (tsohuwar Twitter).

Gwamnatin tarayya ta ce ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a shafukan sada zumunta saboda karya dokoki.
Hoton waya da ke nuna shafukan sada zumunta, da wani rike da waya, da Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kokarin tsabtace shafukan sada zumunta

Wannan mataki na gwamnati ya fito ne daga rahoton bin Dokar CoP ta 2024 da masu gudanar da dandalan sadarwa irin su Google, Microsoft, da TikTok suka miƙa wa gwamnati, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Isra'ila a Najeriya: Gumi ya ce a fara tsammanin kashe shugabanni Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fitar da dokar CoP ne bisa haɗin gwiwar Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA), da Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC).

Rahoton na 2024 ya bayyana yadda kafofin sada zumunta ke ƙoƙarin kare jama’a daga illolin amfani da intanet.

A wata sanarwa da daraktar hulɗa da jama’a na NITDA, Hajiya Hadiza Umar, ta fitar a ranar Laraba, gwamnati ta ce an goge wallafe wallafe 58,909,112 daga shafuka daban daban saboda karya doka.

Hajiya Hadiza Umar, wadda ta yaba wa Google, Microsoft da TikTok kan ci gaba da bin ƙa’idar amfani da dandalan sadarwa, ta kuma bayyana cewa an shigar da ƙorafe-ƙorafe 754,629 na shafuka ko abin da suka wallafa.

Amfanin rahoton shafukan sada zumunta

Ta ƙara da cewa an goge wallafe wallafe 420,439 da ake ganin sun saba da ka'ida, amma daga baya aka sake ɗora su a shafukan sakamakon ƙorafin da mawallafan suka yi.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Tashar TVC News ta rahoto Hajiya Hadiza Umar tana cewa:

“Rahotannin bin ƙa’idar suna bayar da muhimman bayanai kan yadda shafukan sada zumunta ke ƙoƙarin magance matsalolin tsaro ga masu amfani da su, bisa ƙa’ida da dokokin al’umma na waɗannan kafafen.
“Miƙa wa gwamnati waɗannan rahotannin na nuna wani gagarumin mataki wajen samar da ingantacce da kuma amintaccen yanayi na amfani da yanar gizo ga ‘yan Najeriya."

Ta ƙara da cewa:

“Hakan na nuna jajircewar waɗannan shafukan sada zumuntar wajen tabbatar da tsaro da amincewar jama’a a yanar gizo.”
Hukumar NiTDA ta ce za ta ci gaba da kare 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta
Wasu daga cikin shugabannin NITDA a lokacin da suke gudanar da taro a ofishin hukumar da ke Abuja. Hoto: @NITDANigeria
Source: Twitter

Za a kare 'yan Najeriya a soshiyal midiya

Daraktar ta ce wannan na zuwa ne bayan dokar da ta wajabta wa manyan shafukan sadarwa yin rijista a Najeriya tare da bin dokokin kasar, ciki har da biyan haraji, yayin da ake ƙarfafa tsaro a yanar gizo ga ‘yan kasar.

“Yayin da NITDA ta yaba da waɗannan ƙoƙari, muna jaddada cewa samar da ingantaccen yanayi na amfani da yanar gizo na buƙatar haɗin kai na tsakanin duk masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

“Za mu ci gaba da aiki tare da masana’antu, ƙungiyoyin farar hula da hukumomi don ƙara inganta matakan tsaro, haɓaka ilimin amfani da yanar gizo, da kuma bunƙasa amincewa da gaskiya a cikin tsarin fasahar zamani na Najeriya.”

- Hajiya Hadiza Umar.

Tinubu ya nada shugaban NITDA

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sababbin nade-nade a ma'aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani.

Tinubu ya nada sababbin shugabanni a hukumomin NIPOST, NCC, NITDA, NIGCOMSAT da NDPC domin inganta sasdarwa da tattalin arziki.

Shugaban kasar ya amince da nadin Kashifu Inuwa Abdullahi a matsayin shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Najeriya, watau NITDA.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com