Gwamnatin Buhari ta na so a kawo dokoki a kan amfani da shafukan sada zumunta

Gwamnatin Buhari ta na so a kawo dokoki a kan amfani da shafukan sada zumunta

  • Majalisa ta saurari ra’ayoyin mutane a kan kiran yi wa dokar NBC garambawul
  • Minista ya bada shawarar kafa wasu dokoki wajen aiki da shafukan yanar gizo
  • Lai Mohammed yana so a rika bibiyar duk abubuwan da ake yi a irinsu Twitter

Jaridar Leadership ta ce Gwamnatin tarayya ta na cigaba da kokarin ganin an tsabtace abubuwan da ke yawo a kafofin sada zumunta da shafukan yanar gizo.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da su bada dama ayi taka-tsan-tsan da abubuwan da ke yawo a yanar gizo.

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana matsayar gwamnati ne yayin da ake sauraron kudirin neman yi wa dokokin hukumar NBC garambawul a majalisar tarayya.

KU KARANTA: Gwamnati ta na nuna alamar lokacin da za a dawo aiki da Twitter

Ministan yana so majalisar wakilan Najeriya ta bada damar a rika bibiyar duk wasu kafofin sada zumunta na zamani, ana kokarin tace sakonnin da su ke yawo.

The Cable ta rahoto Ministan yana cewa:

“Ina so in yi karin bayani na musamman a nan, ya kamata a sa kafofin yanar gizo da shafukan sada zumunta a jerin nan. Domin aikinmu ne mu rika duba abubuwan da ke yawo, har da shafin Twitter.”

Mohammed ya ambaci sunan dandalin Twitter karara, inda a yanzu gwamnati ta dakatar da kamfanin.

Ministan yada labarai da al’adu na kasa
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun shirya zama da Gwamnatin Najeriya - Twitter

Kwamitin yada labarai da bayanai na majalisar wakilan tarayya ya shirya wannan zama, inda ake sauraron ra’ayoyin jama’a a kan yi wa aikin NBC kwaskwarima.

A halin yanzu masu ruwa da tsaki suna neman majalisa ta rage karfin NBC, sannan a ba hukumar damar cin gashin kanta, ba ta zauna a karkashin Ministan labarai ba.

Kafin yanzu gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta taba kawo maganar a kawo dokar da za ta yi aiki a kan yadda ake amfani da dandalin zamani da yanar gizo.

Kwanan na Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ya ce Twitter da mamallakinta, Jack Dorsey, suna da alhaki a rikicin #EndSARS da aka yi.

A lokacin da wannan rigima ta barke, kasar nan ta tafka asarar dukiya. Lai ya ce Jack Dorsey ya bude asusun gudumawa ga masu zanga-zangar da ta zama rikici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng