Daga zuwa Neman Kudi, 'Yan Najeriya Fiye da 7,000 Sun Maƙale a Ƙasar Libya

Daga zuwa Neman Kudi, 'Yan Najeriya Fiye da 7,000 Sun Maƙale a Ƙasar Libya

  • Shugabar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa ‘yan Najeriya 7,000 da suka fita neman kudi sun makale a kasar Libya
  • Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron kaddamar da tsarin aiki na hukumar kula da ci-rani ta duniya (IOM)
  • Shugabar IOM, Ms. Sharon Dimanche, ta ce tsarin da aka kaddamar bayan shawarwarin ‘yan Najeriya, zai taimaka wa 'yan ci-rani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce ‘yan Najeriya 7,000 sun makale a ƙasar Libya.

Dabiri-Erewa ta bayyana haka ne a bikin ƙaddamar da tsarin aiki na hukumar kula da ci rani ta duniya (IOM) ga Najeriya na shekarar 2025-2027, a Abuja.

Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce 'yan Najeriya 7,000 sun makale a Libya
Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa tana jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @nidcom_gov
Source: Twitter

'Yan Najeriya 7000 sun makale a Libya

Kara karanta wannan

Gwamnati ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

A daren ranar Talata, jaridar The Nation ta ruwaito Dabiri-Erewa tana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A halin da ake ciki yanzu, ‘yan Najeriya fiye da 7,000 sun makale a Libya. Har yanzu akwai masu zura kasashen nan ci rani a ƙafa.”

A jawabinta na maraba, shugabar hukumar IOM a Najeriya, Ms. Sharon Dimanche, ta bayyana cewa an samar da tsarin aikin IOM ga Najeriya don amfanin ‘yan kasar.

Ta ce:

“Mun yi zama, ƙarƙashin jagorancin ministan jin kai, kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, muka duba wannan tsari. Muna so IOM ta zama hanyar ci gaba a gare ku.
“Na zo ƙasar nan domin mu zauna mu yi aiki tare da juna. Duk wani tsari da kuka gani ya fito ne daga tunani da shawarwarin ku, ƙarƙashin jagorancin kwararrun da muka yi aiki tare da su.

IOM ta nemi hadin kan 'yan Najeriya

Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen kiran gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wajen ganin an aiwatar da tsarin IOM din gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

"Kan mage ya waye": Jam'iyyar PDP ta kada hantar APC, ta fadi abin da zai faru a 2027

Ta ce:

“Ba ma so a ce an ƙaddamar da tsarin an bar shi a haka, da wannan nake kira ga kowa da kowa da mu zo mu yi aiki tare wajen aiwatar da shi. Ina fatan nan da shekara uku zuwa biyar, za mu ga amfanin hakan ga 'yan ciranin mu.
“Muna so mu ga canji, kuma ina da yakinin cewa hakan za ta tabbata ne da goyon bayan ku."
Hukumar IOM ta yi magana kan muhimmancin tsarin da ta bullo da shi a Najeriya
Jami'an hukumar IOM na ba da agaji ga 'yan ci rani a Afrika. Hoto: @UNmigration
Source: Twitter

Ministoci da gwamnoni za su tallafa wa IOM

A sakonta na fatan alheri, mataimakiyar daraktar IOM, Ugochi Daniels, ta ce:

“Duk da ce akwai tarin kalubale, amma da IOM da kuma haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin Najeriya, za mu kai ga nasara.”

Karamin Ministan jin kai, Yusuf Sununu; Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim; shugaban sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa; da wakilan jihohin Borno, Yobe, Abia, Bauchi da wasu sun yi alƙawarin tallafawa aiwatar da tsarin IOM.

An taso keyar 'yan Najeriya 109 daga Libya

Kara karanta wannan

'Ya cancanci tazarce,' An ba ƴan Najeriya dalilai 20 na sake zabar Tinubu a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta karɓi ‘yan Najeriya 109 da suka maƙale a birnin Tripoli na ƙasar Libya.

Hukumar kula da ‘yan ci rani ta duniya (IOM) ce ta taimaka wajen dawo da waɗanda aka kwaso zuwa Najeriya.

Rukunin waɗanda suka dawo sun haɗa da mata manya 46, yara biyu, jaririya guda ɗaya, maza manya 52, yara huɗu, da jarirai maza guda huɗu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com