Tallafin Wankin Koda: Gaskiya Ta Fito kan Zargin Tinubu da Ware Kano, Jihohin Arewa 5

Tallafin Wankin Koda: Gaskiya Ta Fito kan Zargin Tinubu da Ware Kano, Jihohin Arewa 5

  • Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta ce ba gaskiya ba ne cewa an ware marasa lafiya daga Arewa maso Yamma a shirin rage kudin wankin koda
  • Sabon shirin ya rage farashin kudin wankin koda daga N50,000 zuwa N12,000 a asibitocin tarayya.
  • Gwamnatin tarayya ta ce za a kara fadada shirin zuwa sauran asibitoci don tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da aka bari a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa marasa lafiya daga yankin Arewa maso Yamma ba sa cikin shirin tallafin gwamnati na rage kudin wankin koda.

Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan bayanin ba shi da tushe, domin an tsara shirin ne saboda kowa da kowa a dukkanin yankunan ƙasar.

Kara karanta wannan

"Sojoji ba za su iya murkushe yan bindiga a jihohi 7 ba," Gwamna ya tsage gaskiya

Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Ali Pate.
Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Ali Pate. Hoto: Federal Ministry of Health
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da ma'aikatar ta yi ne a cikin wani sako da hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, manufar gwamnati ita ce ceton rayuka da rage matsalar lafiya da tattalin arziki ga masu fama da cututtukan koda musamman waɗanda ke cikin ƙalubale na rayuwa.

Yadda aka rage kudin wankin koda

A bisa tsarin da aka amince da shi, gwamnati ta rage farashin kudin wankin koda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal a manyan asibitocin tarayya.

Wannan mataki, a cewar Ma’aikatar, na ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Ana ganin wannan sauki zai taimaka wajen samar da sauƙin kula da marasa lafiya masu fama da cutar koda, tare da bunƙasa damar samun kulawar lafiya ga kowa.

Punch ta wallafa cewa ma’aikatar ta ce wannan yunƙuri wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi domin faɗaɗa tsarin inshorar lafiya ga ’yan ƙasa gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa

Asibitoci 11 da ake aiwatar da shirin

A matakin farko na shirin, gwamnati ta fara aiwatar da shi a manyan asibitoci 11 da ke cikin kowane yanki na ƙasar ciki har da Arewa ta Yamma mai jihohi 6. Asibitocin sun haɗa da:

1. Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

2. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri

3. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi

4. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos

5. Babban Asibitin Ƙasa, Abuja

6. Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Ebute Metta

7. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan

8. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin

9. Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Yenagoa

10. Asibitin Koyarwa ta Tarayya, Owerri

11. Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Abakaliki

Ma’aikatar ta jaddada cewa wannan tsari zai ci gaba da faɗaɗa zuwa sauran asibitoci na tarayya a duk faɗin ƙasar.

Kofar shiga asibitin koyarwa na Aminu Kano
Kofar shiga asibitin koyarwa na Aminu Kano. Hoto: Aminu Kano Teaching Hospital
Source: Twitter

Gwamnati ta ce shirin ya shafi kowa

Ma’aikatar Lafiya ta bayyana cewa ba za a bar wani ɗan Najeriya a baya ba wajen samun damar yin wannan muhimmin aiki na kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Gidaje miliyan 2.2 za su samu kudi a sabon shirin tallafin gwamnatin Tinubu

Ta ƙara da cewa gwamnati na nan daram wajen rage nauyin cututtukan da ba sa yaduwa kamar su cutar koda, domin kare lafiyar al’umma da kuma inganta walwalar jama’a.

Sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa duk wani mai bukata zai samu damar yin wankin koda a farashi mai rahusa a asibitocin gwamnati.

Gwamnati za ta raba tallafi ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya na shirin raba tallafi ga gidaje sama da miliyan 2 a fadin kasar nan.

Karamin minstan jin kai, Honarabul Tanko Sununu ne ya bayyana haka yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.

Ministan ya bayyana cewa shirin na cikin kokarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi domin saukaka rayuwa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng