Gwamna Ya Dauki Shawarar Majalisa, Ya Dakatar da Ciyaman da Jami'an Gwamnati 2
- Gwamna Hyacinth Alia ya amince da dakatar da shugaban karamar hukumar Otukpo, da wasu manyan jami'an gwamnati biyu
- Sanarwa daga gwamnatin jihar Benue ta nuna cewa dakatarwar ta kwanaki 30 za ta fara aiki daga yau Litinin, 20 ga Agusta 2025
- A baya majalisar dokokin jihar ta ƙi tantance wasu kwamishinoni saboda Gwamna Alia ya ƙi dakatar da jami'an gwamnatin uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue – A ranar Laraba, Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya amince da dakatar da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar su uku.
Majalisar dokokin jihar Benue ce ta ba Gwamna Hyacinth Alia shawarar dakatar da jami'an gwamnatin uku, bayan binciken da ta yi.

Source: Twitter
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna, Kula Tersoo, ya fitar ga manema labarai, inji jaridar The Guardian.
Alia ya dakatar da jami'an gwamnati 3
Sanarwar ta ce wadanda abin ya shafa sun haɗa da shugaban hukumar kula da ilimin firamare ta jihar (SUBEB), Dr. Grace Adagba.
Sauran su ne shugaban karamar hukumar Otukpo, Mr. Maxwell Ogiri; da kuma sakataren zartarwa na hukumar kula da harkokin caca ta jihar Benue, Mr. Michael Uper.
A cewar sanarwar, dakatarwar da ta fara aiki tun daga yau, za ta ɗauki tsawon wata guda ne kacal.
Kula Tersoo ya sanar da cewa:
“A bisa shawarwarin da majalisar dokokin jihar Benue ta bayar, mai girma gwamna ya amince da wadannan matakai:
"Dakatar da shugaban karamar hukumar Otukpo, Mr. Maxwell Ogiri, na tsawon wata guda daga yau.
"Dakatar da shugaban hukumar SUBEB, Mrs. Grace Adagba, na tsawon wata guda daga yau.
"Dakatar da sakataren hukumar kula da harkokin caca ta jihar Benue, Mr. Michael Uper, na tsawon wata guda daga yau.”
Rikicin gwamna da majalisar Benue

Kara karanta wannan
Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa
A lokuta daban-daban a baya, majalisar dokokin jihar ta bada shawarar a dakatar da jami’an gwamnatin uku na tsawon watanni shida, amma gwamna bai amince da shawarar ba.
Sakamakon haka, majalisar ta ƙi amincewa da kwamishinoni takwas da gwamna ya tura domin tantance su a matsayin 'yan majalisar zartarwar jihar.
Kuma majalisar ta yi rantsuwar cewa ba za ta sake bi ta kan kowace wasiƙa daga bangaren zartarwar jihar ba, har sai gwamna ya amince da shawarwarin da ta bayar.

Source: Facebook
Matsayar gwamna kan aiki da gaskiya
Jaridar Punch ta rahoto Gwamna Alia ya sake jaddada jajircewarsa wajen bin doka da oda, bin ka’ida, da kuma kiyaye tsarin raba madafun iko.
Ya kuma yaba wa majalisar jihar saboda gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, tare da tabbatar wa jama’ar jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki a bisa gaskiya da riƙon amana
Gwamnan ya bukaci dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da ci gaban ayyukansu ba tare da tangarda ba har zuwa karewar wa'adin dakatarwar shugabanninsu.
Gwamna Alia ya kori kwamishinoninsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya kori dukkanin kwamishinoninsa tare da naɗa shugaban ma’aikata kawai.
An nada Barista Moses Atagher da ya taba rike kwamishinan shari’a da kuma shugaban bankin FMB, a matsayin sabon shugaban ma’aikatan.
Gwamna Alia ya sanar da korar kwamishinonin da kuma naɗin Atagher a ƙarshen taron majalisar zartarwar jihar karo na 12 a birnin Makurdi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

