Karfin Hali: An Cafke Mata kan Barazanar Garkuwa da kuma Hallaka Shugaba Trump

Karfin Hali: An Cafke Mata kan Barazanar Garkuwa da kuma Hallaka Shugaba Trump

  • An cafke wata mata a kasar Amurka da ta yi barazana ga Shugaba Donald Trump a kafar sadarwa ta yanar gizo
  • Matar mai suna Nathalie Rose Jones daga Indiana ta shiga hannu a Washington D.C. bisa zargin shirya sacewa da kashe shugaban kasa
  • Lauyan gwamnatin tarayya ya bayyana cewa ta wallafa barazanar a kafar sadarwa inda ta ce za ta yi kisan domin daukar fansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Hukumomin tsaro a Amurka sun dauki tsattsauran mataki kan wata da ta yi wa Shugaba Donald Trump barazana.

An cafke Nathalie Rose Jones mai shekara 50 daga Lafayette, Indiana a ranar 16 ga Agusta, 2025 a Washington D.C.

An cafke matar da ta ce za ta hallaka Trump
An tura Nath Jones asibiti saboda duba ƙwaƙwalwarta bayan barazana ga Trump. Hoto: Nath Jones, Donald J Trump.
Source: Facebook

An cafke mata kan yiwa Trump barazana

Ana zargin ta shirya “sacewa da kashe” shugaban kasa, Donald Trump domin daukar fansa kan rasa rayuka a Amurka, cewar rahoton Fox News.

Kara karanta wannan

Daga zuwa Umrah, hukumomin Saudi sun cafke 'Yar Kano bayan alakanta jakarta da wiwi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na cikin sanarwar ofishin Lauyan Gwamnatin Tarayya na yankin Columbia da aka wallafa ranar 18 ga Agustan 2025 da muke ciki.

Jones ta yi barazana a Facebook da Instagram wanda aka goge yanzu, inda ta rubuta cewa za ta ka kashe Shugaba Trump domin daukar fansa.

Musabbabin yiwa Trump barazana a Amurka

Hukumar tsaro ta SSS ta fara bincike bayan gano Jones ce marubuciyar wadannan sakwanni da ke dauke da barazana.

A lokacin hira ranar 15 ga Agusta, ta amince da barazanar, inda ta ce za ta yi kokarin kashe shugaban idan ta samu dama, domin daukar fansa kan rayukan da suka salwanta a lokacin cutar COVID-19.

An yi barazanar kashe Donald Trump a Amurka
Shugaba Donald Trump yayin kamfen a Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Twitter

Nath Jones ta janye barazana ga Trump

Daga baya ta janye, ta ce ba ta da niyyar cutar da shi yanzu kuma komai ya wuce kamar ba a yi ba, Global News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

Jones na fuskantar tuhumar yin barazana ga rayuwar shugaban kasa da kuma aikawa da sakonnin barazana ta hanyoyin sadarwa.

Wadannan sakwonni dukkansu laifuffukan tarayya ne wanda kowanensu ke iya jawo hukuncin shekaru biyar a kurkuku.

Lauyan tarayya Jeanine Pirro ta jaddada cewa:

"Barazana ga rayuwar shugaban kasa na daga cikin manyan laifuffuka da za su fuskanci hukunci mai tsanani da ba sassauci."

Zargin da ake yiwa matar a Amurka

Rahotanni sun nuna cewa Jones na fama da matsalar tabin hankali, wanda ma ta amince da shi a shafinta na sada zumunta na zamani.

A halin yanzu, babu wata shaida ta bayyana wane lauya yake kare ta a kotu yayin ake tuhumarta kan manyan laifuffuka a Amurka.

Amurka ta koka kan matsaloli a Najeriya

Kun ji cewa kasar Amurka ta nuna damuwa kan tsaro da kuma yadda ake gudanar da shari’a a Najeriya, musamman zargin tsare mutane ba tare da hukunci ba.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ana ɗaukar matakai wajen gyara tsarin shari’a, ƙarfafa tsaro da kuma gyara tattalin arziki don rage matsin rayuwa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da Bola Tinubu ya yarda da shi ba zai wadatar ba saboda raguwar darajar Naira.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.