Ko Me Ya Yi Zafi: Gwamna Namadi Ya Kori Hadiminsa daga Mukaminsa

Ko Me Ya Yi Zafi: Gwamna Namadi Ya Kori Hadiminsa daga Mukaminsa

  • Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yanke hukuncin korar daya daga cikin masi ba shi shawara na musamman
  • Umar Namadi ya sallami, Rabi'u Garba Kaugama daga kan mukaminsa na mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar tarayya
  • Bayan korar hadimi nasa, an kuma umarce shi da ya dawo da dukkanin kayayyakin gwamnati da ya san suna hannunsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya sallami daya daga cikin hadimansa daga kan mukaminsa.

Gwamna Umar Namadi ya kori mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar tarayya, Rabi’u Garba Kaugama.

Gwamna Namadi ya kori hadiminsa
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, a wajen wani taro Hoto: @aunamadi
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kakakin ofishin sakataren gwamnatin jiha, Ismaila Ibrahim Dutse, ya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025.

Gwamna Namadi ya dawo da kwamishinansa

Kara karanta wannan

Bayan fitowa daga komar EFCC, Tambuwal ya sha alwashi kan gwamnatin APC

A kwanakin baya, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa, ya dawo da kwamishinansa da ya dakatar daga kan bakin aikinsa.

Gwamna Umar Namadi ya dawo da kwamishinan ayyuka na musamman, Danladi Auwalu Sankara, bayan ya dakatar da shi bisa zargin yin lalata da matar aure.

An dai dawo da kwamishinan ne domin ya ci gaba da aikinsa bayan kotu ta wanke shi daga zargin da ake yi masa.

Meyasa Gwamna Namadi ya kori hadiminsa?

Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da ya sanya Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin korar hadimin nasa ba.

A cikin sanarwar, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa korar da aka yi wa Rabiu Garba Kaugama, za ta fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.

"Da wannan ci gaba, an janye dukkan hakkoki da fa'dodi da ke tattare da ofishinsa a matsayin mai ga wa gwamna shawara na musamman kan harkokin majalisar tarayya."

- Isma'ila Ibrahim Dutse

Haka kuma, sanarwar ta umarci tsohon mai ba da shawarar ga Gwamna Namadi da ya mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsa nan take zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

Gwamna Namadi ya sallami hadiminsa
Hoton gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi a cikin ofis Hoto: @aunamadi
Source: Facebook

Karanta wasu labaran game da gwamnan Jigawa

APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta gudanar a mazabar tarayya ta Garki/Babura.

An ji cewa 'dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Mukhtar Rabi'u Garki, ya samu nasarar lashe zaben bayan ya samu kuri'u 38,449.

'Dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP, Auwal Isah Manzo, ya zo na biyu a zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Agustan 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng