Kudin Data, Kira Za Su Yi Sauki, Tinubu Ya Dakatar da Harajin 5% na Kamfanonin Sadarwa
- Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da harajin kashi 5 na kamfanonin sadarwa domin rage yawan kuɗin da ake zuka
- Hukumar NCC ta tabbatar da cirewar, tana mai cewa hakan zai karfafa cigaban masana’antar sadarwa da kare mabukata
- Haka nan gwamnati ta shirya fitar da rahoton ingancin cibiyoyin sadarwa da kuma karin tsare-tsare na kare hakkin masu amfani
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da cire harajin kashi biyar cikin 100 na kamfanonin sadarwa a Najeriya.
Hakan na cikin kudirin da aka gabatar na dokar haraji duba da yawan kudin kira da data da ake ja wanda yan Najeriya ke korafi kansu.

Source: Facebook
Hukumar NCC ta ce Tinubu ya cire harajin 5%
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Dakta Aminu Maida, ne ya tabbatar da cire harajin a lokacin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, cewar Punch.

Kara karanta wannan
ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027
Wannan matakin na daga cikin sababbin sauye-sauyen haraji da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin rage matsin lambar kudi da ‘yan kasa ke fuskanta.
Ya ce an dakatar da shi tun farko, amma yanzu an share shi gaba ɗay inda a cewarsa, wannan wani mataki ne na nuna tausayi ga ‘yan Najeriya.
Tun da farko, an fara gabatar da harajin a cikin shekarar 2022 a lokacin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, sai dai hakan ya jawo adawa sosai daga jama’a.
A watan Yuli 2023, Shugaba Tinubu ya dakatar da shi saboda damuwar yadda zai shafi farashin kudi da cigaban tattalin arziki.
Maida ya bayyana cewa cire wannan haraji zai rage radadin farashi ga masu amfani da wayoyi da kuma karfafa ci gaban masana’antar sadarwa.
Ya ce hukumar za ta fitar da taswirar jama’a a watan Satumba wacce za ta nuna ingancin sadarwa, saurin sauke bayanai da kuma jinkirin sadarwa.

Source: Twitter
Tsare-tsaren da aka samar domin ci gaban sadarwa
Haka kuma za a rika wallafa rahoto kowane wata uku domin ƙara gaskiya da daukar alhakin duk wani lamari da ya biyo baya.
Maida ya kara bayyana cewa tsare-tsare kamar kammala binciken NIN-SIM, warware bashin USSD, da kuma kirkirar tsarin rahoton manyan matsaloli akwai ci gaba.
Wannan, a cewarsa, zai taimaka wajen gina kamfanonin sadarwa masu inganci da karɓuwa a duniya.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta fi karkata yanzu wajen samar da yanayi na haɗin kai a fannin sadarwa na intanet, fasahar zamani, da kare hakkin masu amfani da su.
A karshe, hukumar NCC ta shawarci ‘yan Najeriya su rage shan data da bayanai ta hanyar kashewa, share manhajoji da ba a amfani da su, wannan zai taimaka musu wajen sarrafa kudi da bayanai cikin sauki.
Bankuna: NCC ta dakatar da cire harajin USSD
Kun ji cewa Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta dakatar da cire kudin amfani da wayar hannu don hada-hada, wato USSD daga asusun banki.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya amince da kashe N16.7bn bayan ambaliyar ruwa ta yi barna a Neja
Ana ganin NCC ta dauki matakin ne domin kawo karshen koken kamfanonin sadarwa na cewa bankuna na hana su hakkinsu.
Bankin UBA ya tabbatar wa kwastomomi cewa sabon tsarin ya fara aiki, tare da bayani kan yadda za a ci gaba da mu’amala ta USSD.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
