Bayan Karbe Filaye, Wike Ya Kwace Motocin Mutane Sama da 700 a Abuja

Bayan Karbe Filaye, Wike Ya Kwace Motocin Mutane Sama da 700 a Abuja

  • Hukumar FCTA ta kwace motoci sama da 700 saboda laifuffukan da suka shafi amfani da lambar mota ta jabu da gilashi mai duhu
  • FCTA ta ce mafi akasarin masu fashi da makami a kan hanyar Abuja da ake kira one-chance na amfani da gilashi mai duhu
  • Amma hukumar ta ce shirinta na "Tsaftace Abuja" ya rage fashin one-chance yayin da aka gargadi direbobi kan karya dokokin tuki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar FCTA ta bayyana cewa ta kwace motoci sama da 700 saboda laifuffuka irin su amfani da lambar mota ta jabu da sanya gilashi mai duhu.

FCTA ta ce masu ababen hawar sun karya dokokin zirga-zirga, kuma kama motocin wani sabon mataki ne na kawo karshen aikata laifuffuka a Abuja.

Ma'aikatar birnin tarayya Abuja (FCTA) ta kwace motoci 700 saboda wasu laifuffukan hanya
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a cikin ofishinsa a Abuja. Hoto: @OfficialFCTA
Source: Twitter

FCTA ta kwace motoci 700 a Abuja

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An hana motocin Dangote wucewa a jihar Edo

Daraktan sashen tsaro na FCTA, Adamu Gwary, ne ya bayyana hakan yayin wani shirin binciken ababen hawa a Apo-Wassa da kuma hanyar Karu, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwary wanda ya samu wakilcin sakataren cibiyar umarni da sa ido, Dr. Peter Olumuji, ya bayyana cewa wannan matakin shi ne zagaye na biyu na aikin “Tsaftace Abuja.”

Ya ce an kaddamar da shirin Tsaftace Abuja domin rage fashi da makami na “one-chance” da kuma kwato motocin da aka sace.

“A halin yanzu a aikin Sweep, mun kwace motoci sama da 700. Wannan aikin ya rage yawan fashin one-chance ƙwarai da gaske.
“Muna kira da babbar murya ga duk wani dan ta’adda da ya sani cewa ba inda zai boye mana a Abuja, za mu shiga har inda yake mu kamashi."

- Adamu Gwary.

Wike: Hukuma ta fadi dalilin kwace motoci

Daraktan ya bayyana cewa bayanan sirri da aka samu daga wadanda aka yi wa fashin one-chance sun nuna cewa mafi yawan motocin da ake amfani da su ana sanya masu gilashi mai duhu, kuma ba su da rajista, ko kuma suna dauke da lambobin mota na jabu.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Adamu Gwary ya gargadi direbobi, musamman masu motocin haya, da su guji amfani da gilashi mai duhu, yana mai jaddada cewa masu laifi na amfani da su ne wajen boye ayyukansu.

Ya ce:

“Mun lura akwai wasu masu motocin haya da ke amfani da gilashi mai duhu.
“Mafi yawan wadanda suka fada tarkon one-chance, idan aka tambaye su, sai su ce motar da suka shiga tana da gilashi mai duhu."
Ma'aikatar FCTA ta ce za ta ci gaba da kamen motocin da suka karya dokoki domin tsaftace Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja. Hoto: Legit.ng
Source: Original

DRTS ta yi magana kan laifuffukan hanya

Ita ma shugabar sashen ayyuka na hukumar kula da zirga-zirgar hanya (DRTS), Deborah Osho, ta ce kwamitin hadin gwiwar Sweep ya kara kaimi wajen kawar da motocin haya marasa rajista da marasa launin da doka ta tanadar.

Ta bayyana cewa an kwace wasu motocin saboda laifuffukan zirga-zirga da suka hada da tuka mota a kan hanya ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da lambobin mota na jabu.

Dukkan jami’an biyu sun tabbatar da cewa za a ci gaba da wannan aiki har sai an tsaftace titunan Abuja, inji rahoton PM News.

Wike ya kwace filayen manyan 'yan siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu manyan kasar nan, ciki har da gwamnoni, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tujudeen sun rasa filayensu a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Benue, an hallaka bayin Allah

Ministan harkokin birnin Abuja, Nyesom Wike ya kuma ba da umarnin kwace filayen wasu tsofaffi da kuma masu rike da mukamai a majalisar tarayya.

Wike ya bayyana cewa an dauki matakin ne saboda mutanen sun yi kunnen kashi wajen biyan kudin mallakar filayensu a Abuja kafin wa'adi ya cik.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com