'Gwamnan CBN na Iya Fin Shugaban Kasa Albashi,' Gwamnati za Ta Kara wa Jami'ai Kudi

'Gwamnan CBN na Iya Fin Shugaban Kasa Albashi,' Gwamnati za Ta Kara wa Jami'ai Kudi

  • Hukumar raba kudin shiga ta RMAFC ta bayyana shirinta na duba albashin manyan jami’an gwamnati a Najeriya tun daga tushe
  • Shugaban hukumar, Mohammed Shehu da ya bayyana haka, ya ce albashin shugaban ƙasa da ministoci bai dace da nauyin da ke kansu ba
  • Sai dai tuni kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta yi adawa da shirin, tana mai cewa akwai nuna son kai matuka a al'amarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Hukumar kula da Rarraba Kudin shiga ta bayyana cewa tana shirin sake duba albashin manyan masu riƙe da mukaman gwamnati a Najeriya.

Hukumar ta bayyana albashin da ake biya yanzu a matsayin tsohon tsarin da bai dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar da kuma ƙarin nauyin da ke kan masu rike da mukaman siyasa ba.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun tona yadda wasu ke daƙile kokarin Tinubu kan farashin shinkafa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Hotunan Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban RMAFC, Mohammed Shehu, ya bayyana haka a ranar Litinin, ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu na karɓar albashin N1.5m a kowane wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

RMAFC ta faɗi albashin ministocin Najeriya

Mohammed Shehu ya ƙara da cewa ministocin gwamnati na amsar ƙasa da N1m a kowane wata, kuma wannan albashi bai canja ba tun daga shekarar 2008.

Ya bayyana damuwarsa da cewa:

“Kana biyan shugaban ƙasar Najeriya N1.5m a wata, alhali ƙasar na da mutane sama da miliyan 200. Kowa ya san cewa wannan wasa ne."
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa, Tinubu yayin jawabi a wani taro a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Ya ci gaba da cewa:

“Ba za ka biya minista ƙasa da N1m tun daga 2008 ka ce ya yi aiki da gaskiya ba tare da shiga wasu abubuwan ba. A yau ana iya biyan gwamnan CBN ko wani Darekta Janar ninki 10 albashin shugaban ƙasa. Wannan ba daidai ba ne. Har ma akwai shugabannin hukumomi da ke karɓar ninki 20 na albashin babban lauyan gwamnati (AGF). Wannan kuwa ba adalci ba ne.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin rage bashin N4trn ga kamfanonin wutar lantarki

NLC ta yi watsi da shirin karin albashi

Sai dai kungiyar ƙwadago ta ƙasa ta nuna adawa da shirin RMAFC na ƙara albashin manyan jami’an gwamnati.

Kungiyar ta ce shirin ya yi watsi da ƙara taɓarɓarewar arzikin ƙasa, tare da bayyana cewa sanin kowa ne akwai wasu alawus da jami'an ke mora.

Amma a wani taron manema labarai a Abuja, shugaban RMAFC ya jaddada cewa hukumar ba ta da ikon saita mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Mohammed Shehu ya ce amma kundin tsarin mulki ya ba hukumarsa damar ƙayyade albashin jami’an siyasa, na shari’a da na majalisa.

Ya ce:

“Mun takaita ne kan jami’an siyasa – gwamnoni, sanata, ’yan majalisa, ministoci, DGs da sauran su."

Dalilin gwamnati na ƙin biyan albashin N70,000

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Borno kare kanta saboda rashin fara biyan mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Bola Tinubu ta amince a fara ba ma'aikata.

Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Modu Alhaji Mustapha, ya ce jinkirin ya biyo bayan yawan ma’aikata ƙananan hukumomi.

A jihar Borno, akwai ƙananan hukumomi 27 da ke da kusan ma’aikata 90,000 — adadi mai yawa idan aka kwatanta da wasu jihohin da su ka fara biyan N70,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng