Yara Sun Dauko Bam ba Tare da Sani ba a Borno, Mutane Sun Rasa Rayukansu
- Wani bam da aka dauko daga bayan gari bisa rashin sani ya tarwatse a yankin karamar hukumar Konduga ta jihar Borno
- Rahotanni sun nuna cewa wasu yara ne suka dauko bama-damai ba tare da sani ba, daya daga ciki ya tashi da su yau Litinin
- Rundunar yan sanda ta samu nasarar kwance wani bam da aka gano a gonar wani manomi, ta ja kunnen mazauna yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Aƙalla mutane biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar bam da ta auku a ƙaramar hukumar Konduga, Jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa mutum hudu sun samu raunuka sakamakon fashewar bam din a yau Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.

Asali: Original
Yadda yara suka dauko bama-bamai a Borno
Leadership ta tattaro cewa wasu yara su shida da ke harkar gwangwan ne suka dauko bama-bamai ba tare da sani ba, a tunaninsu karafa ne da za su sayar su samu kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa yaran su na kan hanyarsu ta zuwa Ajari, wani kauye a cikin ƙaramar hukumar, lokacin da ɗaya daga cikin bama-baman ya fashe.
"Mutane biyu suka rasa rayukansu nan take lokacin da abin ya fashe, yayin da huɗu daga cikinsu ke samun kulawa a Asibitin Gwamnati na Konduga,” in ji wata majiya.
'Yan sanda sun gano bam a gonar manomi
Haka zalika, rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta gano wani bam da aka dasa bai kai ga fashewa ba (UXO) a wata gona a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an gano shi ne bayan wani manomi mai suna Babagana Kachalla ya kai rahoton wani abu da ya gani a gonarsa.
A cewarsa, bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Naziru Abdulmajid, an tura tawagar ƙwararrun masu kwance (EOD), inda aka gano cewa bam din Cluster Bomb Unit (CBU) ne mai tsawon mita 2.2 da fadin santimita 30.
Yadda aka kwance bam a gona a jihar Borno
"A bisa ƙa’idar aikin dakarun EOD, an killace wurin yadda ya kamata, daga nan aka binciko inda aka birne mahadar bam din, su ka warware shi cikin nasara," in ji shi.
Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa an wayar da kan al’ummar yankin game da hatsarin bama-bamai domin sanin matakan da za su dauka idan suka ci karo da irin waɗannan abubuwa.

Asali: Getty Images
Rundunar yan sanda ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kare lafiyar al’ummar Jihar Borno, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
“Ana shawartar jama’a da su kasance masu kula, kuma su gaggauta kai rahoton duk wani abu ko motsi da suka zaci abin tuhuma ne ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa,” in ji Daso.
Yan sanda sun tare bama-bamai a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun yi nasarar dakile yunkurin shiga da bama-bamai da makamai cikin jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa an yi yunkurin safarar makaman zuwa Kaduna ta cikin kayan gwangwan amma dakarun yan sanda suka damke su.
Lamarin ya tayar da hankula, musamman ganin yadda ake shigo da kaya daga yankunan da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng