Zaben 2027: INEC Ta Fara Rajistar Masu Kada Kuri'a a Jihohi 36 da Abuja

Zaben 2027: INEC Ta Fara Rajistar Masu Kada Kuri'a a Jihohi 36 da Abuja

  • Hukumar INEC ta sanar da fara rijistar masu kada kuri’a a kasa baki ɗaya daga yau Litinin 18 ga watan Agusta, 2025
  • Ana iya yin rajista ta yanar gizo kafin a fara rajistar kai tsaye a ofisoshin jihohi da kananan hukumomi daga 25 ga Agusta
  • Peter Obi ya yi kira ga ’yan Najeriya su mallaki PVC don yaƙar rashawa da tabbatar da sahihiyar dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta kaddamar da rijistar masu kada kuri’a ta kasa baki ɗaya daga yau Litinin 18 ga watan Agusta, 2025.

Hakan ya fara ne da tsarin rajistar farko ta yanar gizo, kafin a buɗe wajen yin rajista a ofisoshin hukumar na jihohi da kananan hukumomi daga ranar 25 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Zaɓen cike gurbi: Yadda 'yan sandan Kano su ka kama 'yan daba sama da 100

Shugaban hukumar zabe yana bayani wa jama'a a wani taro.
Shugaban hukumar zabe ta kasa yana bayani wa jama'a a wani taro. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Hukumar INEC ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a X a daidai lokacin da aka shirin zabuka masu zuwa, musamman na 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsarin rajistar da hukumar INEC ta sanar

INEC ta bayyana cewa za a gudanar da rajistar kai tsaye a dukkan ofisoshinta na jihohi 36 da kuma a ofisoshin kananan hukumomi 774 a fadin kasar.

Rijistar za ta kasance ga sababbin masu jefa kuri’a masu shekaru 18 zuwa sama, wadanda ke son sauya wurin karɓar PVC da kuma wadanda suka rasa ko lalata katin zabensu.

Hukumar ta gargadi jama’a da su guji yin rijista fiye da sau ɗaya, tana mai cewa hakan zai iya janyo musu hukunci na doka.

Muhimmancin mallakar katin zabe

INEC ta jaddada cewa rajistar kuri’a muhimmin mataki ne wajen tabbatar da shigar kowa cikin harkokin zabe.

Ta kara da cewa kowane ɗan kasa mai cancanta zai sami damar yin rajista, ta hanyar shiga shafin ta a nan ko kuma ta hanyar kiran cibiyar wayar da kai ta hukumar.

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa wakilin PDP duka kan zarginsa da rike musu katunan zabe

Wannan ya nuna jajircewar hukumar wajen tabbatar da cewa babu wanda aka tauye masa damar kada kuri’a a zaben da ke tafe.

Katin zabe: Kiran Peter Obi ga ’yan Najeriya

A gefe guda, tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tabbatar da mallakar katin zabe (PVC) a matsayin makamin tabbatar da adalci.

A sakon da ya wallafa a X, Obi ya ce PVC ne muryar jama'a, kariya ga talakawa, da kuma tsani zuwa ga sabuwar Najeriya da ake fata.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Ya gargadi jama’a da su guji sayar da kuri’unsu, yana mai cewa wadanda ke sayen kuri’u ba su yi hakan don alheri ba, sai dai don su samu damar wawure dukiyar jama’a.

Obi ya yi nuni da cewa wadanda ke sayen kuri’a sukan yi hakan ne domin samun riba daga kujerar mulki, ba don su yi wa jama’a hidima ba.

Kara karanta wannan

Fasinjoji 58 sun gamu da matsala, an hana su shiga jirgin sama a Abuja

An yi gargadi kan magudi a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa dattijon Arewa, Hakeem Baba Ahmed ya gargagi 'yan siyasa da su kaucewa yin magudin zabe a 2027.

Dr. Hakeem Baba ya bayyana cewa magudin zabe a 2027 zai iya jawo babban rikici da zai shafi hadin kan Najeriya.

Legit ta rahoto cewa dattijon ya ce bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali kan walwalar 'yan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng