Asiri ya tonu: An bankado yadda aka rinka sayen kuri'a akan N1K zuwa N7K a zaben Ondo

Asiri ya tonu: An bankado yadda aka rinka sayen kuri'a akan N1K zuwa N7K a zaben Ondo

- Wata kungiyar farar hula, YIAGA Afrika, ta yi Allah-wadai da hauhawar sayen kuri'u da aka yi a zaben gwamnan jihar Ondo

- A ranar 10 ga watan Oktoba, 2020 ne hukumar INEC ta gudanar da zaben jihar Ondo, inda dan takarar jam'iyyar APC ya lashe zaben

- Sai dai kungiyar YIAGA Afrika ta ce babban takaicin shi ne yadda aka rinka sayen kuri'un akan idanuwan jami'an tsaro ba tare da sun cafke masu yi ba

Wata kungiyar farar hula, YIAGA Afrika, ta yi Allah-wadai da hauhawar sayen kuri'u da aka yi a zaben gwamnan jihar Ondo a ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

Kungiyar ta ce babban abun damuwar shi ne yadda aka rinka sayen kuri'un akan idanuwan jami'an tsaro ba tare da sun tsawatar ba.

Shugaban kungiyar YIAGA Afrika, Samson Itodo, ya bayyana hakan a lokacin da ya ke jawabi a cikin wani shirin Talabijin a Abuja, a safiyar ranar Litinin.

KARANTA WANNAN: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye

Asiri ya tonu: An bankado yadda aka rinka sayen kuri'a akan N1K zuwa N7K a zaben Ondo
Asiri ya tonu: An bankado yadda aka rinka sayen kuri'a akan N1K zuwa N7K a zaben Ondo - @MobilePunch
Asali: Twitter

Itodo, wanda ya bayyana cewa YIAGA Afrika ta rarraba jami'anta don sa ido guda 646 a ranar zaben, ta ce "Irin sayen kuri'un da aka yi a zaben ya daga mana hankali."

Ya bayyana cewa, "Ma damar aka ce wai ana zabe ne tsakanin mai kudi da mai kudi, to ba zabe ake yi ba, cinikayya ake yi, kuma hakan barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria.

"A zaben ranar Asabar, an rika sayen kowacce kuri'a akan N1,000 da N7,000 a jihar."

KARANTA WANNAN: Sakon Atiku Abubakar ga matasan Nigeria bayan rushe rundunar FSARS

A cewar Itodo, "Za ka je rumfar zabe ka ga kamar kasuwa, ana sayen kuri'u, kuma gaban jami'an tsaro, suna kallo ba tare da sun hana ba, ko sun cafke su ba.

"Hakan na nuni da cewa mun karbi sayen kuri'u hannu biyu biyu, mun cusa shi a tsarin zaben mu, kuma hakan abun takaici ne."

Shugaban YIAGA Afrika, ya kuma jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bisa nasarar da ta samu na gudanar da zaben lami lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel