'Yan Kasuwa Sun Tona Yadda wasu ke Daƙile Kokarin Tinubu kan Farashin Shinkafa

'Yan Kasuwa Sun Tona Yadda wasu ke Daƙile Kokarin Tinubu kan Farashin Shinkafa

  • Shugaban kungiyar manoma ta AFAN ya ce akwai manoma da dillalai da ke ɓoye shinkafa don tayar da farashi
  • Ya bayyana cewa duk da gwamnati tana bayar da tallafi ga manoma, akwai wadanda ke hana ruwa gudu
  • Sai dai Legit ta samu rahoton cewa a kasuwar Singa da ke garin Kano, farashin shinkafa ya sauko zuwa N60,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Wasu daga cikin shugabannin ƙungiyar manoman shinkafa a Najeriya sun dora alhakin tashin farashinta a kan wasu manoma marasa gaskiya da kuma dillalai.

Mataimakin shugaban ƙasa na All Farmers Association of Nigeria (AFAN), Mista Sakin Agbayewa, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin gwamnati, ana iya samun tashin farashin shinkafa.

Ana zargin manoma da ɓoye shinkafa
Hotunan shinkafa tsaba da ta cikin buhu Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban manoman shinkafar ya bayyana haka ne a tattaunawa da manema labarai da ya yi a Legas a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Tinubu ya sake tausayawa al'umma, zai fara raba kuɗi ga yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin manoma da ɓoye shinkafa

Agbayewa ya ce duk da cewa gwamnati ta bai wa wasu manoma tallafi da ragin 75% na kuɗin sarrafa shinkafa, tare da ba da takin zamani kyauta, akwai shakku ko waɗanda aka tallafa sun yi noma da gaske.

A cewarsa:

"Game da tashin farashin shinkafa, ina ganin muna mayar da hannun agogo baya. Gwamnati ta yi rangwame ga wasu kamfanoni don shigo da shinkafa a farashi mai sauki."

Ya kara da cewa akwai wata ƙungiya da ke neman karya ƙoƙarin gwamnati ta hanyar ɓoye shinkafa a rumbuna, sannan da zarar mai sauƙi ta kare, sai tsawwala farashi.

An samu saukin farashin shinkafa a Kano

Sai dai a karin bayani da ya yi wa Legit Hausa, Sakataren yaɗa labaran kasuwar Singa, Bashir Madara, ya ce babu wani dalili na tashin farashin shinkafa a yanzu

Farashin shinkafa ya sauka a Kano
Hotunan buhunan abinci a wani rumbun adana hatsi Hoto: Bahati
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa:

"Babu dalilin da zai sa shinkafa ta tashi, hasali ma akwai kayan bila-adadin a ƙasa, na mu na gida da kuma wacce ake shigo da ita." Bashir ya ce mafi yawan masu ajiye shinkafa don jiran farashinta ya hau sun shiga nadama saboda sauƙin farashi da aka samu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin rage bashin N4trn ga kamfanonin wutar lantarki

A kalamansa:

"Wasu da yawa sun sayi shinkafar nan N80,000 sun ajiye, amma yanzu ana magana da farashin N60,000 ko ma ƙasa da haka."

A kan batun shigo da shinkafa zuwa Najeriya, Bashir Madara ya ce ba don bude iyakar kasar nan ba, da talaka ya shiga mawuyacin hali fiye da yadda ake tsammani.

Ya ce buɗe iyakokin Najeriya domin shigo da shinkafa alheri ne, Sannan ya yi kira ga gwamnati ta karya farashin kayan noma a Najeriya.

Farashin buhun shinkafa ya sauko

A baya, kun ji cewa wani bincike ya nuna cewa farashin buhun shinkafa (mai kilo 50) ya sauka daga N80,000 zuwa N58,000 a wasu yankuna na Najeriya, musamman karkara.

Rahoton S&P Global ya bayyana cewa Indiya ta fitar da tan miliyan 5.35 na shinkafa zuwa Yammacin Afrika a shekarar 2024, kuma da yawansa ya shigo Najeriya.

Daga Satumba zuwa Disamba, Indiya ta fitar da tan miliyan 2.11, fiye da tan 720,000 na shekarar da ta gabata, lamarin da ya sa farashin ya karye a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng