Yaran Turji Sun Shafe Kwanaki Suna Ta'addanci, Sun Kashe Soja bayan Sace Mutane
- ’Yan bindiga da ke biyayya ga shugaban ta’addanci Bello Turji sun kai hare-hare kan al’ummomi a Sabon Birni, Sokoto, tsakanin 14 zuwa 16 ga Agusta
- Hare-haren sun yi sanadin mutuwar mazauna kauyuka, soja da ɗan sa-kai, tare da sace mutane da dama da har yanzu ba a gano su ba
- Kungiyar kare haƙƙin jama’a ta Movement for Social Justice ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki kan tashin hankalin da ya zama barazana ga rayuwar jama’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Rahotanni daga karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, sun bayyana cewa ’yan bindiga masu biyayya ga shahararren shugaban ta’addanci Bello Turji sun kai hare-hare.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kai hare haren ne kan kauyuka da dama tsakanin ranar Laraba 14 zuwa Juma’a 16 ga watan Agustan 2025.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar jama’a, ciki har da soja da wani ɗan sa-kai, yayin da daruruwan mutane suka shiga rudani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hare-haren da yaran Bello Turji suka kai
Shaidun gani da ido sun ce a ranar Laraba, ’yan bindigan sun yi kwanton ɓauna ga matafiya a hanyar Yankasuwa zuwa Masawa, inda suka tare motoci suka kwashe fasinjojin gaba ɗaya.
Wani wanda ya tsira daga harin ya bayyana cewa sun rika dukan mutanen da ke cikin motocin, lamarin da ya bar jama’a cikin firgici da rudani.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya sanya matafiya a yankin cikin tsananin fargaba da rashin tabbas kan lafiyar su.
Wuraren da aka kai miyagun hare-hare
Punch ta wallafa cewa a ranar Alhamis, ’yan bindigan da ke biyayya ga Turji sun kutsa kauyen Garki, inda suka yi awon gaba da mutum 16.
Daya daga cikin mazauna yankin ya mutu, wani ya arce, yayin da suka kuma kwashe shanun kauyen guda uku.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
Harin ya ci gaba a ranar Juma’a lokacin da suka farmaki kauyukan Turtsawa da Faru da ke kusa da Sabon Birni.
Sun sace mutum 28 daga kauyukan, lamarin da ya bar iyalai cikin tashin hankali suna neman ’yan uwansu da ba su dawo ba.

Source: Facebook
Kiran kungiyar kare haƙƙin jama’a
Kungiyar Movement for Social Justice ta bayyana cewa rahotanninta sun tabbatar da kai hare haren cikin kwana hudu zuwa biyar ba tare da kakkautawa ba.
Kungiyar ta bayyana cewa, duk da ikirarin tattaunawar zaman lafiya, hare-haren Turji da mabiyansa sun ci gaba da yiwa jama’a barna.
A cikin sanarwarta, ta bukaci gwamnatin Sokoto da ta aiwatar da shawarwarin da suka gabatar don kawo ƙarshen kisan gilla da ta kira “barna marar iyaka” da ke ci gaba a yankin.
Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya tabbatar da cewa har yanzu Turji yana cikin jerin masu laifi da ake nema ruwa a jallo.
An kama mai taimakon 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wani boka da ake zargi yana taimakon 'yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin mutumin da aka kaman boka ne da ke ba 'yan ta'addan maganin kariya daga harbi da sauransu.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa za ta cigaba da kokari wajen yaki da masu hada kai da 'yan ta'adda a fadin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

