Kebbi, Neja Za Su Fuskanci Ambaliya, NiMet Ta Yi Hasashen Ruwa Mai Yawa a Arewa
- Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa da zai iya haddasa ambaliya a wasu jihohin Arewa ta yamma da Arewa ta Tsakiya ranar Asabar
- Kebbi da Neja na cikin wuraren da NiMet ta yi gargadin ambaliya, tare da shawartar mazauna su dauki matakan gaggawa ko su kaura daga yankunan
- A lokaci guda, ma’aikatan NiMet na yajin aiki kan karancin albashi, suna korafin halin kunci da matsalolin lafiya da suka addabi yawancinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen cewa ruwan sama mai yawa zai sauka a jihohin Arewa a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.
Sakamakon yawan ruwan da zai sauka, NiMet ta ce za a iya samu ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Kebbi da Neja a ranar ta Asabar.

Source: Getty Images
Gargadin ambaliyar na kunshe ne a cikin rahoton hasashen yanayi da NiMet ta fitar a shafinta na X a yammacin ranar Juma'a, 15 ga Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce duk abin da aka gani a cikin rahoton zai yi aiki ne daga karfe 12:00 na safiya har zuwa karfe 11:59 na daren ranar Asabar.
Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa
A safiyar Asabar, NiMet ta ce za a iya samun ruwan sama a jihohin Jigawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, Zamfara, da Kebbi.
A yammacin ranar kuwa, NiMet ta ce za a ci gaba da samun ruwan a jihohin Zamfara, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi, Gombe da Taraba States.
Sai dai NiMet ta ce ruwan sama mai karfin gaske hade da tsawa da iska na iya sauka a jihohin Borno, Yobe, and Adamawa States.
Sakamakon ruwan sama mai yawa da zai sauka ne hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kebbi.
Hasashen yanayi a jihohin Arewa ta Tsakiya
Idan aka leka Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar ta ce ruwan sama zai sauka a Birnin tarayya Abuja da jihohin Plateau, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, da Niger.
Hukumar NiMet za a fara sheka ruwan sama a Arewa ta Tsakiya tun daga safiya har zuwa daren ranar Asabar.
Sakamakon mamakon ruwan saman da za a sha ne hukumar ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Niger.
Hasashen yanayi a jihohin Kudu
Rahoton NiMet ya nuna cewa za a samu ruwan sama a jihohin Anambra, Imo, Abia, Ondo, Ogun, Edo, Oyo, Lagos, Cross River, Rivers, da Akwa Ibom a safiyar Asabar.
A yammacin ranar kuwa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a jihohin Oyo, Osun, Edo, Ondo, Ogun, Ekiti, Abia, Imo, Delta, Ebonyi, Rivers, Lagos, Bayelsa, Akwa Ibom, da Cross River.

Source: Original
Shawarwarin da hukumar NiMet ta bayar

Kara karanta wannan
'Yan sanda: "Yan siyasa a kano sun yi alkawarin hana zubar da jini a zaben cike gurbi"
Hukumar NiMet ta shawarci wadanda ke zaune a yankunan da suka saba fuskantar ambaliya da su dauki matakin gaggawa ko su kaura daga wuraren.
An kuma shawarci hukumomi da jami'an al'umma da ma masu ruwa da tsaki su zama a cikin shirin ko ta kwana na yiwuwar ambaliya a wannan rana.
Duba rahoton a kasa:
Ma'aikatan NiMet sun shiga yajin aiki
A wani labarin a can baya, mun ruwaito cewa, ma’aikatan NiMet sun fara yajin aiki, inda suka rika zagaye filayen jiragen sama don tabbatar bin umarnin.
Ma’aikata hukumar hasashen yanayin sun koka da karancin albashi, suka ce wasu suna karɓar rance don biyan kuɗin haya da kudin makarantun 'ya'yansu.
Yayin da jagoran masu yajin aikin, Paul Ogohi ya ce ma'aikatan NiMet na mutuwa kamar kaji, ya ce 70% na fama da hawan jini, 90% na da matsalolin ido.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

