Faskari da Sunayen Wasu Ƙananan Hukumomi 2 da Ƴan Bindiga Suka Addaba a Katsina
- Gwamnatin Katsina ta ce kashi 87% na kananan hukumomi sun samu cikakken tsaro, inda suka tsira daga hare-haren ’yan bindiga
- Rahoton tsaron jihar ya nuna cewa kananan hukumomi 12 sun samu tsaro, yayin da wasu tara suke da matsala a wasu kauyuka
- Sai dai, rahoton ya nuna cewa kananan hukumomin Faskari, Kankara da Matazu ne ke cikin matsananciyar barazanar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnatin Katsina karkashin Mallam Dikko Umaru Radda ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a yaki da matsalar tsaro a jihar.
A cewar wani rahoto daga ofishin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, kananan hukumomi uku ne har yanzu 'yan bindiga ke addaba.

Source: Facebook
Matsalar tsaro a garuruwan Katsina
Sabon mai tallafawa Gwamna Dikko Radda kan fasahar sadarwa da kafofin watsa labarai na zamani, Jamil Isma'il Mabai ya fitar da rahoton a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin rahoton, gwamnatin Katsina ta sanar da cewa karamar hukumar Safana ta shiga sahun kananan hukumomin jihar da suka kubuta daga sharrin 'yan bindiga.
Ya zuwa ranar Juma'a, 15 ga watan Agusta, 2025, kananan hukumomi 12 ba su fuskantar wata barazana ta tsaro, yayin da 'yan bindiga suka daina kai hari gaba daya.
Jamil Mabai ya ce cikakken rahoton tsaro daga kananan hukumomi 24 ya nuna cewa kananan hukumomi 3 ne kacal ke karkashin hare-haren 'yan ta'adda.
Ga abin da rahoton ya nuna a kasa:
Kananan hukumomi 12 da ke da tsaro
Rahoton ya nuna cewa kananan hukumomi 12 sun samu tsaro, inda mazauna cikinsu ke rayuwa ba tare da fargabar hari daga 'yan bindiga ba.
Kananan hukukomin su ne: Jibia, Batsari, Dammusa, Katsina, Batagarawa, Charanchi, Bindawa, Ingawa, Kafur, Danja, Kusada, da Safana.
A baya an yi ta fama da matsaloli sosai musamman a irinsu kauyukan Safana da Batsari.

Kara karanta wannan
Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa
Kananan hukumomi 9 masu saukin matsalar tsaro
Hakazalika, rahoton ya ce akwai kananan hukumomi tara da ke fuskantar matsalar tsaro a wasu kauyuka, amma duk da haka, ana samu ci gaba a samar da tsaro a garuruwan.
Kananan hukumomin su ne: Malumfashi, Kurfi, Dutsinma, Kankia, Musawa, Bakori, Funtua, Sabuwa, Dandume.
Sai dai wasu masu bibiyar shafin Malam Mabai sun koka cewa har gobe ana kai hare-hare a a yankin Malumfashi da kewaye.
Kananan hukumomi 3 mafi matsalar tsaro
To sai dai, kamar yadda aka fada a farkon rahoton, kananan hukumomi uku ne ke cikin matsanancin matsalar tsaro, inda 'yan bindiga ke yawan kai masu hare-hare.
Yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin kawo karshen kashe-kashe a wannan garuruwa, rahoton ya nuna cewa matsalar tsaro ta yi kamari a cikinsu.
Kananan hukumomin da abin ya shafa su ne, Faskari, Kankara, Matazu, kamar yadda bayanin ya nuna.

Source: Original
Me wannan rahoton yake nunawa?
A bisa wannan rahoto, gwamnatin Katsina ta ce kashi 87 na kananan hukumomin jihar sun samu cikakken tsaro ko kuma sun samu tsaro sosai.
A kananan hukumomin Faskari, Kankara da Matazu da matsalar tsaron ta yi kamari kuwa, akwai bukatar gwamnati ta dauki matakai masu tsauri kan 'yan ta'adda.
Wannan ya nuna irin kokarin gwamnatin jihar na magance tsaro, musamman idan aka duba rahoton da ya nuna cewa jihar ta kashe N36bn a samar da tsaron.
Duba rahoton a nan kasa:
Safana: An yi sulhu da 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu fahimtar juna bayan sake zaman tattaunawar sulhu da yan bindiga a karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
Karamar hukumar ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar yadda aka yi a Jibia, Batsari, da Danmusa, domin samar da zaman lafiya.
Yarjejeniyar ta ba manoma damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali, yayin da Fulani ke zuwa kasuwa da asibiti ba tare da tsangwama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

