Fasinjoji 58 Sun Gamu da Matsala, An Hana Su Shiga Jirgin Sama a Abuja

Fasinjoji 58 Sun Gamu da Matsala, An Hana Su Shiga Jirgin Sama a Abuja

  • Wani jirgin kamfanin British Arways ya samu matsalar kofa tun kafin tashinsa daga birnin tarayya Abuja zuwa Landan a kasar Birtaniya
  • Sakamakon wannan matsala ne mahukunta suka hana fasinjoji 58 daga cikin mutanen da suka sayi tikici shiga jirgin saman saboda tsaro
  • Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za a kwashe fasinjojin a gobe Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu fasinjoji 58 sun gamu da cikas yayin da za su hau jirgin sama na kamfanin British Airways daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Landan.

Kamfanin jiragen sama na British Airways a yau ranar Juma’a, ya hana fasinjoji 58 shiga jirgin daga Abuja zuwa London saboda matsalar ƙofa.

Jirgin kamfanin British Airways.
Hoton jirgin kamfanin sufurin British Airways yayin da yake tafiya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Saboda dalilan tsaro, kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa, kamar yadda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta tabbatar a shafn X.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NCAA ta tabbatar da lamarin

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Kwastomomi na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani saƙo da ya fitar yau Juma'a.

Ya bayyana cewa, saboda matsalar ƙofar, “sun tilasta hana fasinjoji 58 shiga jirgin da safiyar Juma'a, 15 ga watan Agusta, 2025.”

“Tuni dai aka samar da masaukin otel, kuma fasinjoji 28 daga ciki sun zabi komawa gidajensu, yayin da 30 suka amince da tayin masaukin da aka masu.
“Fasinjojin da abin ya shafa na iya neman diyya. Ana shirye-shiryen jigilar su zuwa Landan washegari watau ranar Asabae da safe,” in ji shi.

NCAA ta bai wa fasinjojin jirgin sama shawara

Achimugu ya shawarci fasinjoji cewa mataki na farko idan irin wannan ya faru shi ne neman jami’an kare haƙƙin fasinjoji na hukumar NCAA a filin sauka da tashin jirgin.

A cewarsa, ta haka kadai za a tabbatar da cewa an kare haƙƙinku (idan jirgi ya samu jinkiri).

Kara karanta wannan

Jerin manyan kujerun gwamnatin tarayya da Tinubu ya ba mutanen Kano a shekaru 2

Jirgin kamfanin British Airways da jama'a filin jirgin sama.
Jirgin kamfanin British Airways a sama, tare da hotun jama'a na harkokinsu a filin jirgi Hoto: @BritishAirways
Source: Twitter

Ko da yake wannan mataki na tsaro ne, wani mai amfani da kafar sada zumunta ya shawarci NCAA da ta duba yanayin cikin wasu jiragen da kamfanonin waje ke kawo wa Najeriya.

Mutumin mai amfani da Skood009 a shafin X ya yabawa hukumar NCAA, yana mai cewa wannan ne karon farko da ya ga an saurari koken fasinjoji cikin gaggawa.

"Dole mu yaba maka yallabai, wannan ne karon farko da aka saurari korafin fasinjoji yadda ya kamata kuma ta hanyar da ya dace. Ina fatan za a fadada irin haka zuwa wasu sassan gwamnati," in ji shi.

Jirgin kamfanin Rano Air ya samu matsala

A wani rahoton, kun ji cewa jirgin kamfanin Rano Air ya gamu da matsalar inji bayan ya taso daga Kano zuwa jihar Sakkwato a Arewa maso Yamma.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin dakatar da tashi jirgin da aka samu wannan matsala nan take.

An gano cewa injin jirgin saman na farko ya samu matsala yayin da jirgin ke tsaka da tafiya bayan ya baro Kano kafin ya sauka a garin Sakkwato.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262