"Ku Shirya Mutuwa," Charly Boy Ya Fadi abin da Zai Faru da Wasu Ƴan Siyasa a 2027

"Ku Shirya Mutuwa," Charly Boy Ya Fadi abin da Zai Faru da Wasu Ƴan Siyasa a 2027

  • Charly Boy ya gargadi ’yan siyasa cewa duk wanda ya murde zaben shugaban kasa na 2027 ya shirya tunkarar mummunar sakamako
  • Ya bayyana taken 2027 a matsayin "Ka murde zabe, ka mutu," yana mai cewa ’yan Najeriya ba za su sake amincewa da murdiya ba
  • Mawakin ya yaba wa Omoyele Sowore kan fafutukar da yake yi, yana mai cewa ana bukatar irinsu don fadawa gwamnati gaskiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Mawakin Najeriya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Charles Chukwuemeka Oputa ya aika sakon gargadi ga 'yan siyasa gabanin zaben 2027.

Mawakin da aka fi sani da Charly Boy ko kuma Area Fada ya ce 'yan siyasar da ke shirin murde zaben 2027 su shirya tunkarar bala'in da ke tunkaro su.

Charly Boy ya ce 'yan siyasa za su mutu idan har suka yi murdiya a zaben 2027.
Mawakin Najeriya, Charly Boy a lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi a Legas. Hoto: @AreaFada1/X
Asali: UGC

"Ku murde zabe ku mutu" - Charly Boy

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bude sabon shiri, za a hada matasa da masu daukar aiki a duniya

Charly Boy ya yi wannan maganar ne a wata tattauna ta musamman da Rudolf Okonkwo, a shirin 90MinutesAfrica, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawakin da ya saba yin maganganun da ke jawo ce-ce-ku-ce ya ce taken zaben 2027 shi ne "Ka murde zabe, ka mutu," yana mai cewa 'yan Najeriya ba za su kara jure murdiyar zabe ba.

Charly boy ya ce:

"Duk wani dan siyasa da ya shirya murde zaben 2027 to kuwa ya shirya mutuwarsa. Ka murde zabe ka mutu, shi ne taken 2027 kawai.
"Abin da zai faru a kasar nan daga 2027 zuwa 2027 shi ne zai sa 'yan Najeriya su yanke shawarar ci gaba da shan bakar wahala ko kuma kawo sauyin sauya hali a kasar."

Charly Boy ya caccaki gwamnati mai ci

Jagoran na kungiyar OurMumuDonDo ya kuma caccaki gwamnati mai ci a kasar yana mai cewa kuskure ne a ci gaba da kyale "gurbatattun cikinmu" su ci gaba da mulkar "mafi kyawunmu."

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa ya kamata Goodluck Jonathan ya marawa Peter Obi baya a 2027'

Charly Boy ya kuma yi martani kan gwamnatin jihar Legas na sauya sunan tashar motar Bariga daga sunansa, yana mai zargin cewa shiri ne kawai na kawar da tunanin mutane daga abubuwan da ke faruwa.

A cewarsa, damuwarsa ita ce yadda za a ceto miliyoyin 'yan Najeriya daga tsananin talauci, yana mai cewa akwai wadanda ke kwana ba su ci abinci ba.

"Ana iya sauya gurbatacciyar gwamnati a Najeriya ne kawai a ranar da aka fara kada kuri'a. Don haka, dole mu wayar da kan jama'a kan wanda za su zaba a 2027.
"Mun gaji da irin mulkin da ake yi maga. Ba za mu daga kafa ga duk dan siyasar da ya ce zai yi murdiyar zabe a 2027. Ka murde zabe ka mutu kawai."

- Charly Boy.

Charly Boy ya bukaci 'yan Najeriya su fito su kada kuri'ar tsige wannan gwamnati daga mulki a 2027
Fitaccen mawakin Najeriya, Charly Boye ya halarci taron mawaka da aka yi a Legas. Hoto: @charlyboy
Asali: Instagram

"Muna bukatar matasa irinsu Sowore" - Charly Boy

Sahara Reporters ta rahoto mawakin ya kuma yabawa Omoyele Sowore, kan karfin hali da jajurcewar da ya nuna a lokacin da 'yan sandan Najeriya suka kama shi.

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

"Dole ne masu fafutukar neman 'yanci irinsu Sowore su rika fuskantar barazana da kamu daga masu adawa da fafutukarsu. Lallai komai ya lalace a gwamnati.
"Ba abu ne mai sauki fadawa masu mulki gaskiya ba. Muna bukatar irin Sowore a Najeriya. Ni na yi amanna da cewa za a samu sauyi ne kawai idan matasa suka yunkuro da murya daya."

- Charles Chukwuemeka Oputa.

Mawaki Charly Boy ya saka matarsa a caca

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen mawakin Najeriya Charly Boy ya saka matarsa a caca a lokacin da ake dab da zaben shugaban kasar Amurka.

A lokacin zaben, Charly Boy ya sha alwashin sakin matarsa wadda suka shafe shekaru 47 suna tare, ma damar Kamala Harris ba ta ci zabe ba.

A cewar Charly Boy, Amurka ta cancanci samun shugabar kasa mace ta farko kuma bakar fata bayan Barrack Obama, alwashin da ba a ji ya cika ba bayan nasarar Donald Trump.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.