Gwamna Bala Ya Ɗauko Ɗan Ƙasar China, Ya ba Shi Muƙami a Gwamnatin Bauchi

Gwamna Bala Ya Ɗauko Ɗan Ƙasar China, Ya ba Shi Muƙami a Gwamnatin Bauchi

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya nada ɗan ƙasar China, Li Zhensheng, a matsayin mai ba shi shawara game da tattalin arziki
  • Bala Mohammed ya sanar da nadin ne a lokacin da ya kulla yarjejeniya da cibiyar bincike ta CGPCRC da Li Zhensheng ke jagoranta
  • A cewar gwamnan, kulla alaka da cibiyar CGPCRC zai jawo masu zuba jari daga waje, bunƙasa kasuwanci, da inganta rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya nada wani dan kasar China, Mr. Li Zhensheng, a matsayin mai ba gwamna shawara kan tattalin arziki.

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a taron rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Bauchi da cibiyar CGPCRC a jihar.

Gwamnan Bauchi ya nada dan China mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki
Gwamnan Bala Mohammed tare da Mr. Li Zhensheng, dan China da ya ba mukami a Bauchi. Hoto: @DeeOneAyekooto
Source: Twitter

Gwamna Bala ya ba dan china mukami

Mai girma gwamnan ya ce wannan matakin da ya dauka zai sanya Bauchi ta zamo a gaba gaba wajen kulla alaka da kasashen duniya don samar da ci gaba, inji rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

"Ba gudu, ba ja da baya," Naja'atu ta karfafa gwiwar tambuwal bayan kamen EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Mohammed ya ce nadin Li Zhensheng zai yaukaka alakar kasuwanci, bunkasa gine-gine da kuma jawo masu zuba jari daga waje, musamman ma China.

Idan har manufar wannan nadi ta tabbata, to kuwa jihar za ta samu ci gaba a fuskar noma, ilimi, kiwon lafiya, kere-kere, hakar ma'adanai, mai da gas da kuma kasuwanci.

A cikin yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu, an samar da bayanai game da wasu muhimman ayyuka da cibiyar za ta gudanar tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar.

Alakar gwamnatin Bauchi da CGPCRC

Jaridar Punch ta rahoto Gwamna Bala Mohammd ya bayyana cewa:

"A cikin yarjejeniyar da aka cimma, za a kafa ofishin wakilcin Bauchi a China da zai rika kula da ayyukan da za a gudanar da tabbatar da cewa an yi su a kan lokaci."

Gwamnan ya bayyana cewa wannan yarjejeniyar ta yi daidai da tsarin diflomasiyya tsakanin Shugaba Xi Jinping na China da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

A cewarsa, wannan alakar da gwamnatin Bauchi ta kulla da cibiyar CGPCRC za ta amfani kasashen biyu, kuma ta kara karfafa dangantakarsu.

"Wannan ba wai yarjejeniya ce don gina ababen more rayuwa ba, har ma da sauya rayuwar jama'a baki daya. Za mu tabbatar cewa mun tallata Bauchi a kasashen duniya."

- Gwamna Bala Mohammed.

Gwamna Bala Mohammed ya ce alakar da ya kulla da dan China za ta jawo wa Bauchi masu zuba jari da ababen more rayuwa
Gwamna Bala Mohammed yana sanya hannu a wasu takardu a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Bauchi. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Kalaman 'dan Chinan ga Gwamna Bala

Gwamnan na Bauchi ya ce kulla irin wannan alakar za ta jawo masu zuba jari daga waje, ya samar da ayyukan yi, bunkasa kwarewar ma'aikata, da daga darajar Bauchi a idon duniya.

A nasa jawabin, Li Zhensheng, wanda shi ne shugaban cibiyar bincike ta China Global Promotion Cooperation, ya yi alkawarin amfani da cibiyar wajen bunkasa tattalin arzikin Bauchi.

"Za mu tabbatar mun yi duk mai yiwuwa wajen tallafawa Bauchi ta cimma muradunta na ci gaban tattali, gina ababen more rayuwa na zamani da kuma samar da ci gaba ga jama'arta."

- Li Zhensheng.

Gwamna Bala ya gana da Peter Obi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Bauchi ya roƙi tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

Sanata Bala Mohamamed ya yi wannan roko ne yayin da ya karbi bakuncin Peter Obi da masoyansa a fadar gwamnatin Bauchi.

A nasa jawabin, Peter Obi ya ce ya ziyarci Bauchi ne domin tattaunawa da ɗaliban kwalejoji da almajirai domin ganin irin tallafin da zai ba su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com