'Karkatar da Kudin Ma'aikata,' NLC Ta Yi wa Gwamnati Barazanar Shiga Yajin Aiki

'Karkatar da Kudin Ma'aikata,' NLC Ta Yi wa Gwamnati Barazanar Shiga Yajin Aiki

  • NLC ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai ta mayar da kudaden ma’aikata da ake zargin ta karkatar daga asusun NSITF
  • Kungiyar ta bayyana karkatar da kashi 40 na kudaden ma’aikata a matsayin keta dokar NSITF da hari ga hakkokin ma’aikata
  • NLC ta kuma bukaci a gaggauta kafa hukumar gudanarwar PENCOM, tana gargadin shiga yajin aiki idan aka gaza daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai ta mayar da kudaden ma’aikata da ake zargin an karkatar daga asusun NSITF.

NLC ta yi Allah-wadai da karkatar da kashi 40 na gudunmawar ma’aikata daga asusun inshorarsu zuwa asusun gwamnatin tarayya.

'Yan kwadago na barazanar shiga yajin aiki saboda zargin gwamnati na karkatar da kudin ma'aikata daga asusun NSITF
Shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero yana jawabi a taron bikin ranar ma'aikata ta kasa a Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

Ana zargin an karkatar da kudin ma'aikata

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar kwadagon ta fitar bayan kammala taron kwamitin CWC a Abuja ranar Laraba, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

"Ba gudu, ba ja da baya," Naja'atu ta karfafa gwiwar tambuwal bayan kamen EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar kwadago ta bayyana karkatar da kudin a matsayin keta dokar kafa asusun inshora na NSITF da kuma kai hari ga hakkokin ma’aikata.

Sanarwar ta ce:

“CWC ta nuna bacin rai kan ci gaba da take hakkin ma’aikata ta hanyar karkatar da kashi 40 na kudin inshorar ma’aikata zuwa asusun gwamnati a matsayin ‘kudi shiga’,wannan keta dokokin kafa NSITF ne.
“Wani abin Allah-wadai kuma shi ne ikirarin karya na wannan gwamnati cewa ita ce mai hakkin mallakar hedikwatar NLC, ginin da ma’aikatan Najeriya suka mallaka."

Ana zargin gwamnati da hantarar 'yan kwadago

Kungiyar NLC ta kuma zargi gwamnatin tarayya da yunkurin boye gyaran da ta ce ake yi wa dokar NSITF ta yadda za a hana ma’aikata hakkokinsu tare da ba gwamnati cikakken iko kan kudaden.

Ta kuma bayyana cewa:

"Hakazalika, abin takaici ne yadda gwamnatin ta ke amfani da kafofin watsa labarai tana yi wa ƙungiyoyin kwadago da shugabanninsu barazana.

Kara karanta wannan

'Akwai sharadi,' Gwamnati za ta fara ba ma'aikatan manyan makarantu bashin N10m

“CWC na gargadin gwamnatin tarayya cewa wadannan matakan hari ne kai tsaye ga hakkokin ma’aikata, dukiyoyinsu da suka sha wahala wajen tarawa, da kuma ka’idar gudanarwar tarraya da aka tanada a ƙa’idodin aiki na duniya."

Kungiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta kafa hukumar gudanarwa ta hukumar fanshon kasa (PENCOM).

Kungiyoyin kwadago sun nemi gwamnati ta kafa shugabannin hukumar PENCOM
Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero tare da mambobin kungiyar suna zanga-zanga kan karin kudin sadarwa a Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

NLC ta nemi a kafa shugabannin PENCOM

A game da PENCOM, Vangaurd ta rahoto kungiyar NLC ta ce:

“CWC ta nuna damuwa kan rashin kafa hukumar gudanarwa ta PENCOM, wanda ya saba wa dokar PENCOM da sauran dokoki
“Wannan gibi ya ba gwamnati damar rike ikon sarrafa kudaden fansho na ma’aikata, ta yadda aka kawar da tsarin kulawar tarraya da doka ta tanada, tare da ƙara fargabar ci gaba da karkatar da kudin a nan gaba.
“CWC na nanata cewa kudaden fansho hakkin ma'aikata ne na wani kason albashinsu da aka ajiye wa, ba kudin shigar gwamnati ba ne, kuma tana bukatar a gaggauta kafa hukumar gudanarwar PENCOM kamar yadda doka ta tanada."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin rage bashin N4trn ga kamfanonin wutar lantarki

Kungiyar NLC ta ƙara da cewa idan ba a dauki mataki ba kafin cikar kwanaki bakwai, NLC za ta tsunduma yajin aikin da ba zai yi wa kowa dadi ba.

NLC ta soki shekaru 2 na mulkin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, NLC ta ce shekaru biyu da Bola Tinubu ya yi kan mulki sun jefa ma’aikata da talakawa cikin ƙarin wahala.

Kungiyar kwadagon ta ce babu wani abin da za a iya murna da shi tun bayan da Tinubu ya hau mulki, face hauhawar farashi da ƙarancin abinci.

NLC ta kuma zargi gwamnatin Bola Tinubu da musgunawa shugabannin ƙwadago da watsi da alƙawuran da aka musu a tattaunawarsu ta baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel