Tinubu Zai Kashe Naira Biliyan 142 a Gina Tashoshin Mota a Kano da Wasu Jihohi 5
- Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da kashe N142.02bn don gina tashoshin bas na zamani a shiyyar jihohi shida
- Yayin da aka ba kamfanin Planet Project kwangilar aikin, an ce za a gina tashoshin a jihohin Abeokuta, Gombe da su Kano
- Ministan sufuri ya ce aikin zai karfafa tsaro, kara jin dadin fasinjoji, tare da kuma bunkasa kasuwanci a shiyyoyin kasar shida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da kashe Naira biliyan 142.02 domin gina sababbin tashoshin bas na zamani a shiyyoyi shida na Najeriya.
Ministan sufuri, Sa’idu Alkali, ne ya sanar da amincewar yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, bayan zaman majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.

Asali: Twitter
Gwamnatin Tinubu za ta gina tashoshi 6

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7
Jaridar The Cable ta rahoto Sa'idu Alkali ya bayyana cewa an ba kamfanin Messrs Planet Project Limited kwangilar gina tashoshin guda shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da za a gina tashoshin su ne kamar haka:
- Abeokuta (Kudu maso Yamma)
- Gombe (Arewa maso Gabas)
- Kano (Arewa maso Yamma)
- Lokoja (Arewa ta Tsakiya)
- Onitsha (Kudu maso Gabas)
- Ewu, jihar Edo (Kudu maso Kudu)
Amfanin gina tashoshin bas a Najeriya
Ministan ya bayyana wannan aikin a matsayin “zuba jari na farko kai tsaye daga gwamnatin tarayya” da ya mayar da hankali kan gine-ginen sufurin kasa, baya ga aikin gina tituna.
Sa'idu Alkali ya ce:
“Duk da rawar da harkar sufurin kasa ke takawa a Najeriya, babu isassun tashoshin bas da aka gina musamman don biyan bukatun miliyoyin fasinjoji.
“Wannan gibi ya taimaka wajen karuwar laifuffuka, hadurran mota, da kuma yaduwar makamai da harsasai a manyan tituna."
Alkali ya ce za a aiwatar da aikin a ma’aikatar sufuri domin karfafa tsaron hanya, kara jin dadin fasinjoji, da kuma inganta harkokin kasuwanci a yankunan shida.
Ya ce sai da aka gama cikakken bincike sannan ne aka gabatar da kudirin ga shugaban kasa da majalisar FEC domin amincewarsu, la’akari da irin amfanin da zai kawo ga harkokin sufuri da tsaro na kasa.
FEC ta kafa sharudda kan sayen kayayyaki
Wannan na zuwa ne yayin da majalisar FEC ta ba da umarnin kammala dukkanin saye da sayar da kayyaki da ke karkashin kasafin kudin shekarar 2024 nan da Satumba, 2025.
NTA News ta rahoto cewa umarnin na daga cikin matakai da aka dauka bayan shugaban hukumar kula da sayen kayayyakin gwamnati (BPP), Adebowale Adedokun ya gabatar da rahoto ga majalisar.
Ministan watsa labarai, Muhammed Idris, ya bayyana cewa FEC ta bayar da umarni shida kan yadda ake gudanar da sayen kayayyaki a gwamnati yayin taron.

Asali: Facebook
Umarnin da FEC ta bayar a taronta
Daga cikin umarnin akwai wanda aka ba ministoci na su tabbatar da cewa an ba da kwangilar dukkanin ayyukansu da ke a kasafin kudin 2025 bisa tsarin dokar bayar da kwangila.
Majalisar ta kuma umurci Ministan kudi da ya tabbatar da cewa shugaban BPP yana cikin tattaunawar nemo rance domin gudanar da ayyukan gine-gine a kasar.
Haka kuma, an umurci kamfanonin gwamnati da cibiyoyin kasuwanci su tabbatar da bin dokar hada-hadar kudi ta shekarar 2020 a dukkan tsarin siyan kayan da suke gudanarwa.
Bola Tinubu zai gina titin jirgi a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na gina layin dogo a cikin birnin Kano, wanda zai lakume Naira tiriliyan 1.5.
Wannan jawabi ya fito daga shugaban kwamitin kasafi na majalisar wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kano.
Hon. Abubakar Bichi ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na jajircewar shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen samar da ababen more rayuwa da bunkasa Arewa baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng