Rai Bakon Duniya: Zababbar Kansila Ta Rasu Kwana 14 Kacal bayan Rantsar da Ita
- Zababbar kansila ta Ibeju-Lekki, Oluwakemi Rufai, ta rasu kwana biyu kafin ta cika makonni biyu da rantsar da ita
- Shugabannin karamar hukuma da APC sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, yayin da aka yabawa da jarumtarta
- Wasu 'yan Najeriya sun nuna alhini kan rasuwar kansilar yayin da wasu suka nuna hadarin shiga cikin harkokin mulki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lagos – Zababbar kansila mai wakiltar Mazabar C1 a karamar hukumar Ibeju-Lekki ta jihar Legas, Oluwakemi Rufai ta rasu.
An rahoto cewa Oluwakemi Rufai ta koma ga mahaliccinta ne kwana biyu kafin ta cika makonni biyu da rantsar da ita a matsayin kansila.

Source: Twitter
Zababbar kansila a jihar Legas ta rasu
Oluwakemi, wacce ita ce kadai ce mace a majalisar karamar hukumar, ta rasu ne a safiyar Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban karamar hukumar Ibeju-Lekki, Sesan Olowa, da shugaban karamar hukumar ci-gaban Lekki (LCDA), Rasaki Kasali, sun tabbatar da rasuwar.
A cikin sanarwa da suka fitar a lokuta daban-daban, shugabannin sun bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga majalisa da al’ummar Lekki.
Jam’iyyar APC reshen jihar Legas, ta hannun mai magana da yawunta, Seye Oladejo, ta bayyana matuƙar bakin cikinta bisa rasuwar Oluwakemi Rufai.
Jam'iyyar APC ta yabi kansilar da ta rasu
Seye Oladejo ya bayyana Oluwakemi Rufai a matsayin “ƙwararriyar matashiya da ta fara shahara a APC” wacce ta mayar da hankali kan haɗa kan mata.
Punch ta rahoto ya ƙara da cewa abubuwan da ta aiwatar a dan karamin lokacin da ta yi a ofis ya nuna jajircewarta wajen cigaban al’umma da biyayya ga manufofin jam’iyya.
Ya mika ta’aziyya ga iyalan kansilar, al’ummar Ibeju-Lekki da mazabarta, yana jaddada cewa “ba za a manta da ayyukanta, sadaukarwa, jarumta da hangen nesanta ba."

Source: Original
Martanin mutane game da rasuwar kansilar
Casmir Y. Hountonnagnon:
"Kamar ba ta yi bincike kafin ta shiga ba. 'Yan siyasa sun riga sun cinye ta."
Chimuanya Prosper:
"Ƙarfinta bai kai ba ne. Idan kana siyasa, dole ka zamo jan wuya sosai ko da kujerar da ka ke a kai ƙarama ce. Yanzu dai sun wancakal da ita gefe. Allah ya jiƙan ta."
Abdullahi Suleiman Bici:
"Allah ya ba iyalanta haƙurin jure wannan rashi."
Sani Ajingi Foundation:
"An harba mata kibiya mai haɗari, ya Ubangiji ka ji ƙanta. Allah ka da ka sa mu yi kuka a lokacin da ya kamata ace muna murna."
Mustapha Agbaje:
"Allah ya jikanAlhaja Rufai, ya kuma albarkaci ‘ya’yan da ta bari."
Ovbiogie Vincent:
"Wani ne zai amfana da wannan mutuwar, kuma da gangan za su zabi wanda bai dace da kujerar ba."
Bivan Shindong Patrick:
"Haba Madam, ba ki fara cin komai ba sai ki tafi ki shiga siyasa? Yanzu ga shi kin gamu da sharrin siyasar."

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka
Freeborn Odjarhe:
"Idan ba za ki iya doke su ba, to ki shiga cikinsu ko ki gudu don tsira da ranki."
Chukwuemeka Ezeakonobi:
"Ubangiji ya ji ƙan ta. Wannan shiyasa nake gaya wa mutane su daina cewa za su goyi bayan dan takara kafin 2027, saboda abu abu daya Allah zai yi ya rusa duk wata makarkashiya."
APC ta lashe zaben ciyamomi a Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 20 a zaɓen kananan hukumomi na Jihar Legas.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Legas (LASIEC) a ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2025 ta bayyana cewa APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 375 cikin 376 a jihar.
Bayanan da aka samu daga LASIEC sun nuna cewa an tantance jam'iyyun siyasa 15 daga cikin 19 da suka yi rajista domin fafatawa a zaɓen ciyamomi da kansilolin Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

