Jami'an NDLEA Sun Kai Samame, an Cafke Masu Safarar Kwayoyi a Kano
- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun kai samame kan wuraren da take zargin ana aikata laifuffuka a Kano
- A yayin da ma'aikatan suka kai samame, sun samu nasarar cafke mutanen da ake da aikata laifuffukan da suka shafi harkar miyagun kwayoyi
- Hazalika NDLEA kwato kala daban-daban na miyagun kwayoyi daga hannun mutanen da ake zargi suna safararsu a jihar Kano
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, ta ce ta kama mutane 49 da ake zargi da aikata laifuffuka.
Hukumar NDLEA ta ce ta kama mutanen ne wadanda ake zargi da aikata laifuffuka masu nasaba da miyagun ƙwayoyi, tare da kwace nau’o’in kwayoyi daban-daban a cikin jihar.

Source: Facebook
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ranar Laraba, 13 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
'Yan sanda: "Yan siyasa a kano sun yi alkawarin hana zubar da jini a zaben cike gurbi"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NDLEA ta yi kamu a jihar Kano
Sadiq Muhammad-Maigatari ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a yayin samamen da aka gudanar a ranakun 7 da 8 ga watan Agusta a wani ɓangare na ƙoƙarin rage yaduwar laifuffukan da suka shafi miyagun kwayoyi.
A cewar Sadiq Muhammad-Maigatari, a ranakun 7 da 8 ga watan Agusta, hukumar ta kai samame a wurare da dama da aka fi sani da gudanar da harkokin miyagun ƙwayoyi.
Ya ce a yayin samamen an kama mutane 34 a Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata, Kofar Wambai, Kofar Dan’agundi, Makabartar Dan’agundi, Ladanai, Zage, da Tashar Rimi a kasuwar Rimi.
"Haka kuma, rundunar ta kai samame a Tashar Kano Line da Tashar Rami a Na’ibawa, inda aka cafke mutane 15."
- Sadiq Muhammad-Maigatari
Ya ƙara da cewa abubuwan da aka samu daga hannun waɗanda aka kama sun haɗa da, tabar wiwi, Pregabalin, diazepam, robar maganin tari mai codeine, Rohypnol, sha ka mutu, man roba da kuma makamai.

Source: Facebook
NDLEA za ta ci gaba da zafafa ayyukanta
Kwamandan hukumar a jihar Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana cewa wannan aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin rusa maboyar masu harkar miyagun ƙwayoyi da katse safarar su a jihar.
Ya yabawa shugaban NDLEA na kasa, Birgediya Janar Mohamed Buba-Marwa, bisa jajircewa da irin jagorancin da yake yi a hukumar.
Abubakar Idris-Ahmad ya yi kira ga masu harkar fataucin miyagun ƙwayoyi da su daina, tare da gargadin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta batar da miyagun kwayoyi a cikin al'umma.
Jami'an NDLEA sun cafke dillalin kwaya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun samu nasarar cafke wani rikakken dillalin miyagun kwayoyi, Okpara Paul Chigozie.
Rikakken shugaban masu safarar miyagun kwayoyin dai ya shiga hannu ne bayan an yi shekara shida ana nemansa ruwa a jallo.
Okpara Paul Chigozoe ya shiga hannu ne lokacin da yake kokarin safarar kayan maye daga yankin Kudu maso Gabas, zuwa wasu sassan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
