‘Yan Fashi 50 Sun Farmaki Kwalejin Bauchi, Barnar da Suka Yi Ta Sa An Rufe Makarantar
- Dalibai 10 sun jikkata bayan ‘yan fashi sama da 50 sun kutsa kai hari cikin kwajelin tarayya ta Bauchi a lokacin da daliban ke barci
- Zanga zanga ta barke a a kofar kwalejin, inda dalibai suka yi kira ga hukumomi da su dauki mataki kan matsalar tsaro a makarantar
- Bayan faruwar hakan, hukumar makarantar ta rufe kwalejin har sai baba ta gani, inda ta umarci dalibai su kwase dukkan kayansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Akalla dalibai 10 ne suka samu munanan raunuka yayin da wasu 'yan fashi dauke da makamai suka farmaki dakin kwanan dalibai a Bauchi.
An ce 'yan fashi da yawansu ya haura 50 sun kutsa cikin kwalejin fasaha ta tarayya da ke Bauchi a safiyar ranar Talata, inda suka sassari dalibai.

Asali: Twitter
'Yan fashi sun farmaki kwalejin Bauchi
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa bayan faruwar lamarin, daliban makarantar sun gudanar da zanga zanga a kofar shiga kwalejin, don nuna bacin ransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daliban sun jawo tsaikon zirga zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa, yayin da suke kira ga hukumomi su dauki matakin gaggawa.
A cewar daliban, 'yan fashin sun farmaki dakunan kwanan dalibai da misalin karfe 2:00 na safiyar Talata, suna nuna wa dalibai bindiga, tare da sarar wadanda suka yi masu turjiya.
Wasu dalibai da suka yi magana da menam labarai sun ce rashin isasshen tsaro ne ya jawo har 'yan fashin suka samu damar shiga cikin kwalejin.
Ta'asar da 'yan fashin suka yi wa dalibai
Masu zanga zangar, wadanda suka ki barin malamai da sauran ma'aikata shiga cikin makarantar, sun ce babu haske a dakunan kwanan dalibai, wanda ke sa wurin ya yi duhu.
Wani dalibi ya bayyana cewa:
"Muna cikin barci muka fara jin hayaniya daga dakunan da ke kusa da mu. 'Yan fashin da suka haura 50 suka farmake mu da bindigogi da adduna, suna magana da Hausa.
"Duk da cewa ba su kashe ko daya daga cikinmu ba, amma sun ji wa wasu dalibai munanan raunuka. Wani har ya samu matsalar kashin gadon baya."

Asali: Twitter
An rufe kwalejin Bauchi bayan harin
Hukumar gudanarwar kwalejin fasaha ta tarayya ta Bauchi ta sanar da rufe makarantar na har sai baba ta gani bayan zanga-zangar daliban da ta barke, inji rahoton The Nation.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata, magatakardar kwalejin, Alhaji Kasimu Salihu ya ce makarantar ta samu rahotannin harin da 'yan fashi suka kai wa daliban.
"Mun fahimci cewa wasu bata gari da ke nufin dalibai da makarantar da sharri sun mamaye wannan zanga zanga tare da kokarin rikidar da ita zuwa wata fitina."
- Alhaji Kasimu Salihu.
Hukumar gudanarwar ta bukaci dukkanin dalibai su fice daga dakunan kwanansu cikin awanni biyu, tana mai cewa dole ta rufe makarantar zuwa wani lokaci gaba saboda matsalar tsaro.
'Yan bindiga sun sace daliban kwaleji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun yi aika-aika a Delta yayin da suka sace wasu dalibai mata masu yin karatu a wata kwalejin ilmi.
Miyagun sun sace daliban ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Asaba, babban birnin jihar Delta domin yin wasu abubuwa.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an sako daya daga cikin matan da aka sace bayan da aka biya miliyoyim kudi a matsayin kudin fansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng